Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP a Wurin Gangamin Atiku

Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP a Wurin Gangamin Atiku

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi dubbannin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP a Adamawa
  • Atiku Ya kai ziyara mahaifarsa a karon farko tun bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP
  • Ziyarar Atikun na zuwa ne yayin da ake kokarin dinke ɓarakar PDP, musamman tsakaninsa da Wike

Adamawa - Jam'iyyar PDP ta karbi dubbannin mambobin jam'iyyu daban-daban da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar a jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne ya karɓi masu sauya shekan a wani taron gangami da ya gudana Yola, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Atiku ya tabbatar musu cewa sun zama ɗaya da kowane mamba kuma ba za'a nuna musu banbanci ba a sabuwar jam'iyyar da suka shiga.

Kara karanta wannan

Zan Yanke Hukunci Kan Ko Zan Fice Daga Jam'iyyar Kwankwaso A Wannan Makon, Shekarau Ya Magantu

Atiku Abubakar.
Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP a Wurin Gangamin Atiku Hoto: Atiku Abubakar/facebook
Asali: Facebook

"Muna tsammanin zaku yi aiki tukuru domin mu samu nasara a zaɓen 2023 da ke tafe," inji Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun da dokar hani kan kamfe tana nan daram, PDP jam'iyya ce mai bin doka da oda kuma zata jira zuwa lokacin da ya dace don buga gangar yaƙin neman zaɓenta.

Tsohon mataimakin shugaban na tsawon zango biyu ya ce ya shiga fafutukar neman kujera lamba ɗaya ne saboda kwaɗayinsa na yi wa al'ummar Najeriya aiki.

"Ziyara ta a yau ba wani abu bane illa na dawo gida saboda na jima ban zo gida ba tun lokacin da na lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP," inji shi.

Ɗan takarar ya yaba wa Gwamna Ahmadu Fintiri bisa nasarorin da ya samu a ɓangaren tsaro, ayyukan raya kasa, ilimi, lafiya da demokaraɗiyyar cikin gida a tsakanin iyalan PDP na jihar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ne Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Tsohon Makusancin Buhari

Ya roki al'ummar Adamawa su cigaba da nuna masa goyon baya domin ya cigaba da zuba musu ayyukan demokaraɗiyya ba tare da nuna banbanci ba ta hanyar samar da walwala tsakanin su.

Su waye suka sauya sheka zuwa PDP?

A taron, Atiku ya karɓi mambobin APC 1,640 da suka sauya sheƙa zuwa PDP daga ƙananan hukumomin Fufore da Mubi.

Da yake jawabi, shugaban PDP a Adamawa, Mr A.T. Shehu, ya ce wasu mambobi sama da 1,600 sun sauya sheƙa daga karamar hukumar Toungo yayin da wasu yan majalisun jiha biyu suka jagoranci wasu zuwa PDP a Mubi da Fufore.

Wani mamban PDP da ya halarci wurin taron gangamin, Abdulrahman Umar, ya tabbatar da batun sauya sheƙar ga Legit.ng Hausa.

A hirrasa da wakilin mu, Ɗan siyasan ya ce dubbannin mutane ne suka yi cincirindo a wurin taron. Ya kara da cewa wasu yan majlisun jiha biyu da masoyan su sun koma PDP a gangamin.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

A kalamansa ya ce:

"Tabbas na halarta dubban mutane ne suka yi cincirin do, kuma akwai yan majalisun jahar adamawa guda biyu wadda suke kan kujeransu suka sauya sheka zuwa PDP tare da magoya bayan su."

A wani labarin kuma Makusancin Ministan Buhari Ya Koma PDP Yayin da Wani Gwamnan Adawa Ya Kulla Ƙawance da APC

Na hannun daman tsohon ministan Sufuri kuma kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, Chris Finebone, ya sauya sheka zuwa PDP.

Wannan cigaban na zuwa ne a lokacin da gwamna Wike na Ribas ya fara ɗasawa da wasu jiga-jigan APC.

Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a shekarar 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya yi karanci Lissafi a digirinsa na farko a jami'ar kimiyya da fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel