Ina Fatan Ku Samu 200: El-Rufai Ga Masoya Peter Obi Masu Shirin Gangamin Mutum Miliyan 2 a Kaduna

Ina Fatan Ku Samu 200: El-Rufai Ga Masoya Peter Obi Masu Shirin Gangamin Mutum Miliyan 2 a Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya bayyana shakku ga manufar magoya bayan Peter Obi na karbuwar dan takararsu a Kaduna
  • Magoya bayan Obi na shirin yin gagarumin taron gangami a Kaduna, inda suke shirin tara mutane sama da miliyan biyu
  • An yi gangamin tattakin nuna goyon bayan Obi a jihohin Nasarawa da Cross River a kwanan nan, an dai ga jama'a a tattakin

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, ya caccaki magoya bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour kan wani yunkuri na yin tattaki tare da mutum miliyan biyu a jihar.

Yayin da zaben 2023 ya rage watanni shida, magoya bayan Obi sun yi tattakin nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Isah Ashiru Kudan Ya Bayyana Muhimman Abubuwa Guda Uku Da Zai Yi Idan Ya zama Gwamnan Kaduna

A kwanakin baya an gudanar da irin wannan tattaki na Peter Obi a jihar Nasarawa da kuma jihar Cross River.

El-Rufai ya zolayi masoya Peter Obi
Ina fatan ku samu 200: El-Rufai ga masoya Peter Obi masu gangamin mutumin miliyan 2 a Kaduna | Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

A Kaduna kuwa, sun bayyana shirinsu na yin wannan tattakin neman goyon baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Umar Zarma, wani dan a mutum Peter Obi ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, za su yi tattakin mai daukar hankali na mutum miliyan biyu a Kaduna.

Sai dai, gwamnan jihar Kaduna bai ga lamarin a matsayin abu mai sauki ba, inda ya zolayi magoya bayan nasa da kalamai masu ban dariya.

Wani yanki na rubutun El-Rufai ya ce:

"A Kaduna? Ba Tuwitan Kaduna ba? -
"Ina fatan ku samu mutum dari biyu akan tituna harda ‘wadanda za su shigo dasu’ da ba za su bude shagunansu a ranar Litinin ba, sun zo a mota a daren jiya!!."

Tashin Hankali a APC Yayin da Jam’iyyar Ta Gaza Mayarwa ’Yan Takarar da Suka Janye Kudin Fom

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jirgin Sojojin NAF Ya Halaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

A bangare guda, watanni hudu bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a mayar wa ‘yan takarar da suka janye daga takarar APC a taron gangami na ranar 26 ga Maris, har yanzu jam’iyyar ba ta bi umarninsa ba.

Bincike ya kuma nuna cewa ‘yan majalisar da suka gudanar da taron na kasa (daga unguwanni zuwa matakin kasa) na bin APC kudade gabanin babban zaben 2023.

Jam’iyyar, a cikin watanni biyun da suka gabata, ta kuma gaza wajen biyan albashin ma’aikata kamar yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel