2023: Shugaban Matasan APC Dayo Israel Ya Fitar Da Bidiyon Tinubu Yana Taro A Karfe Daya Na Safe

2023: Shugaban Matasan APC Dayo Israel Ya Fitar Da Bidiyon Tinubu Yana Taro A Karfe Daya Na Safe

  • Shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya ce Bola Ahmed Tinubu ya kan wuce karfe hudu na safiya bai yi barci
  • Dayo Israel, shugaban matasan jam’iyyar APC, yana yin iyakacin kokarinsa don tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa Tinubu na da koshin lafiyar da zai iya shugabancin Najeriya
  • A cikin jerin rubuce-rubucen da ya yi a kafafen sada zumunta, Dayo yana ta yada labarin cewa komai ya daidaita da Tinubu

FCT, Abuja - A wata ganawa da ya yi da wasu ‘yan Najeriya kwanan nan a birnin Landan, Dayo Isra’ila, shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai kwanta barci da karfe 4 na safe a rana ta farko.

Da yake raba bidiyon a shafinsa na Instagram, Israel ya ce Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, yana da dakunan guda bakwai a gidansa kuma yana shiga daya bayan daya don ganawa da maziyartan sa.

Ya yi tambaya da kakkausar murya inda ya ce:

“Asiwaju baya kwanciya barci kafin karfe hudu na safe, sai ka ce min mutumin nan bai da lafiya? To, ka gaya mani cewa mutumin nan bai dace da shugabanci ba, ko ba shi da kuzari?
Tinubu
2023: Shugaban Matasan APC Dayo Israel Ya Fitar Da Bidiyon Tinubu Yana Taro Da Karfe Daya Na Safe FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bidiyon, da ya saka a shafin na Tuwita mai taken : “Asiwaju ba ya barci kafin karfe 4 na safe. Ya tashi kuma yana aiki na sa'o'i masu yawa yana saduwa da mutane. Yana da kuzarin zama shugaban kasa.

“Ya taba zama a kasashen waje kuma da zai dawo Najeriya, ya dawo da wasu abokan aikinsa gida, don haka ku kwantar da hankalin ku gwamnatin Asiwaju na kowa da kowa ne.

"Yan Najeriya mazauna kasar waje suna da wurin zama a cikin gwamnati Asiwaju.
“Kuma tun lokacin da ya zama gwamna, yake gudanar da bikin godiya na shekara-shekara wanda yake gayyatar manyan fastoci a Najeriya, duk ya bar mulki har yanzu yana gudanar da wannan biki.

Da yake mayar da martani ga da'awar Isra'ila, wasu daga cikin mabiyansa sun musanta furucin nasa. Domin tabbatar da ikirari da ya yi a baya, Isra’ila a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, ya sake yin wani faifan bidiyo na shi da Tinubu a gidan tsohon gwamnan da karfe 1 na safe. Ya wallafa bidiyon a shafin Twitter ya kuma rubuta:

Sanusi: Na Gargadi Gwamnatin Buhari Cewa Manufofinta Za Su Lalata Tattalin Arzikin Najeriya

A wani labari kuma, Jihar Legas - Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sai da ya gargadi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa manufofinta na tattalin arziki za su lalata arzikin Najeriya. Rahoton THIS DAY

Sanusi ya kuma koka da halin da kasar ke ciki, yana mai cewa Najeriya ba za ta sami cigabar da yakamata ba muddin masu rike da mukaman gwamnati basu dauki aikinsu da kima ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel