Sanusi: Na Gargadi Gwamnatin Buhari Cewa Manufofinta Za Su Lalata Tattalin Arzikin Najeriya

Sanusi: Na Gargadi Gwamnatin Buhari Cewa Manufofinta Za Su Lalata Tattalin Arzikin Najeriya

  • Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa ya gargadi gwamnatin Buhari da cewa manufofinta na tattalin arziki za su lalata arzikin Najeriya
  • Halifa Sanusi yace akwai matsala har idan mutanen dake son su jagorance mu baza su iya fadama mana yadda zasu inganta rayuwar mu ba
  • Sanusi yace idan kowane shugaban kasa, gwamna, minista, da kwamishina zai dauki aikin shi da muhimmanci, kasar nan ba za ta kasance inda take ba a yanzu

Jihar Legas - Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sai da ya gargadi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa manufofinta na tattalin arziki za su lalata arzikin Najeriya. Rahoton THIS DAY

Sanusi ya kuma koka da halin da kasar ke ciki, yana mai cewa Najeriya ba za ta sami cigabar da yakamata ba muddin masu rike da mukaman gwamnati basu dauki aikinsu da kima ba.

Kara karanta wannan

Tsigaggen sarki Sanusi ga matasa: Ku gina Najeriya, ku daina guduwa kasashen waje

Tsohon Sarkin, wanda ya yi magana a Legas ranar Lahadi a wani taro duk wani hadari da ke tattare da tsarin tattalin arzikin na sanar da gwamnati lokacin da ta hau mulki a shekarar 2015/2016 wanda ita ce kasar fuskanta a yau.

Tsohon Sarkin Kano ya tuna yadda ya rubuta wasikar sirri ga tsohon shugaban kasa Goodluck a lokacin da yake gwamnan babban bankin Najeriya CBN yana bayyana damuwarsa kan tattalin arzikin kasar.

Sanusi
Sanusi: Na gargadi gwamnatin Buhari cewa manufofinta za su lalata tattalin arzikin Najeriya FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanusi yace idan kowane shugaban kasa, gwamna, minista, da kwamishina zai dauki aikinsu da muhimmanci, kasar nan ba za ta kasance inda take ba a yanzu.

Har idan mutanen dake son zama ministoci, kwamishinoni, gwamnoni da shugaban kasa na tsawon shekaru takwas, ba su gaya mana yadda za su inganta rayuwarmu ba, muna da matsala.

Tsohon gwamnan na CBN ya bayyana dalilin da yake sukar manufofin gwamnati da ya ga akwai matsala, abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne, sai ya shawarci gwamnati a boye na tsawon watanni kafin ya fito fili.

Kara karanta wannan

Babu Nadamar Komai Saboda Tunbuke Ni, Kuma Ba Zan Yi Shiru Ba Inji Sanusi II

Dangane da gwamnati mai ci, Sanusi ya ce ya gargadi gwamnatin tarayya kan illolin da ke tattare da manufofinta a shekarar 2015, musamman yadda za ta lalata tattalin arzikin kasar.

Sanusi ya ce ya dauki shekara 2015 zuwa 2016 yana sanar da su, cewa manufofin tattalin arzikin da suka tsara zai lalata arzikin Najeriya.

Sai da abin ya faskara na yi magana a bainar jama’a, kuma dole ne mu yi magana. Yanzu tambayar da kowa ke yi shine ya kamata sarki yayi magana? Amsar ita ce eh ya danganta da abin da kuke magana akai inji Sanusi.

Yarinya 'Yar Shekara 22 Dauke Da Juna Biyu Ta Ce Tana Son Masoyinta Mai Shekaru 88

A wani labari kuma, Chibalonza tana da shekaru 22, amma zuciyarta ta kamu da son wani mutum mai suna Kasher Alphonse wanda ya isa ya zama kakanta mai shekaru 88. Rahoton Legit.NG

Kara karanta wannan

Sarkin Kano Sanusi: Duk da an tsige ni a sarauta, amma ba zan kame baki game da Najeriya ba

Masoyan sun shafe shekaru biyu suna tare da juna, inda suka ce zukatan su ke soyayya, ba shekarun su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel