Dan Majalisar Wakilai Yakubu Rilisco Ya Fice Daga PDP Ya Dawo APC a Kebbi

Dan Majalisar Wakilai Yakubu Rilisco Ya Fice Daga PDP Ya Dawo APC a Kebbi

  • Bayan shan kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP, dan majalisa ya dawo jam'iyyarsa ta da, jam'iyyar APC
  • Gwamnan jihar Kebbi da sauran jiga-jigan siyasar jihar sun karbi dan majalisar da a baya ya fice daga jam'iyyar APC
  • A karshen makon jiya aka samu wasu 'yan siyasar jihar Kebbi da dama da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC

Jihar Kebbi - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza, Hon Bello Yakubu Rilisco ya ficewarsa daga PDP ya koma ta APC, rahoton TVC.

Dan majalisar na tarayya ya shaidawa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Litinin cewa ya yanke sauya sheka ne saboda muradinsa na hada karfi da karfe da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu domin kai jihar ga wani matsayi mai girma.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Masu fada a ji a PDP mutum 4 sun gaji da jam'iyyar, sun ja magoya bayansu sun koma APC

Dan majalisar APC ya dawo gida bayan komawa PDP
Dan Majalisar Wakilai Yakubu Rilisco Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC a Kebbi | Hoo: tvcnews.tv
Asali: UGC

Relisco dai ya koma PDP ne domin ya tsaya takara a zaben fidda gwani na kujerar da yake kai a halin yanzu, inda ya sha kaye a hannun Barista Bello Halidu, dan tsohon shugaban PDP na kasa.

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“APC jam’iyyata ce kuma na dawo gida kuma na gamsu da irin gagarumin ci gaban jihar da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya kafa a halin yanzu.
"Gwamna Bagudu shugaba ne wanda ya dace da duk wani mai tunani, mai son ci gaban tattalin arzikin jihar da Najeriya ya kamata yayi koyi da shi."

Bagudu na kowa ne, inji Rilisco

Rilisco ya kuma bayyana gwamnan a matsayin mai tawali’u, mai kwarjini, mai jama'a kuma na kowa, rahoton Daily Sun.

A cewarsa:

“Kwazonsa da kyawawan halayensa na shugabanci ne suka haifar da shigowa jam’iyyar APC daga wasu jam’iyyu. Shi mai kishin kasa ne, mai tsoron Allah, mai gaskiya da rikon amana, don haka na zo ne domin hada karfi da karfe da shi don ci gaba da bunkasa jihar.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Samu Babban Tawaya A Yayinda Fitaccen Jigonta Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar

“A nan ina kira ga takwarorina na sauran sassan da su dawo cikin jam’iyyar APC domin ciyar da jihar da Najeriya gaba.”

Rilisco ya bayyana hakan ne a gaban Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kebbi ta Arewa, Alhaji Sahabi Lolo.

Hakazalika da dan majalisar wakilai mai wakiltar Maiyama, Honarabul Umaru Salah, (Yuyu) da kuma hadimin gwamna na musamman Alhaji Faruk Musa Yaro, (Enabo).

Kebbi: Wasu Masu Fada a PDP Sun Ja Magoya Bayansu, Sun Koma Jam’iyyar APC

A wani labarin, wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP hudu a masarautar Zuru ta jihar Kebbi tare da magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, rahoton Daily Sun.

Wadannan jiga-jigai da suka sauya sheka sun hada da Alhaji Shehu Ribah daga Danko/Wasagu; Alhaji Nuhu Goma daga Zuru; Alhaji Adamu Jalalo daga Fakai da Alhaji Babuga Diri daga kananan hukumomin Sakaba na jihar.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Alhaji Samaila Yombe-Dabai, da shugaban jam’iyya a jihar, Alhaji Abubakar Kana-Zuru ne suka tarbe su a wani taro da aka yi a Zuru ranar Lahadi, PM News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel