El-Rufai Ya Sace Gwiwan Kakakin Atiku, Ya Ce Ko Gawarsa Ba Za A Tsinta Kusa Da PDP Ba

El-Rufai Ya Sace Gwiwan Kakakin Atiku, Ya Ce Ko Gawarsa Ba Za A Tsinta Kusa Da PDP Ba

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin ba zai taba shiga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) PDP ba gabanin 2023
  • El-Rufai yana martani ne ga kakakin kamfen din Atiku, Daniel Bwala wanda ya bayyana cewa gwamnan Kadunan zai fita daga APC ya koma PDP kafin zaben 2023
  • Gwamnan Kadunan, amma, ya ce ko gawarsa ba za ta koma jam'iyyar hammaya ta PDP ba a wani martanin da ya yi a Twitter

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi martani kan yiwuwarsa na komawa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

El-Rufai yana martani ne kan ikirarin da kakakin kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023, Daniel Bwala, na cewa tsohon ministan na Abuja zai fice daga APC ya dawo PDP.

El-Rufai
El-Rufai Ya Sace Gwiwan Kakakin Atiku, Ya Ce Ko Gawarsa Ba Za A Tsinta Kusa Da PDP Ba. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shafinsa na Twitter, Bwala, wanda a baya-bayan nan ya fice ya fice daga APC, ya ce yana kyautata zaton El-Rufai zai shiga PDP kafin zaben 2023.

Ya kuma bayyana gwamnan na Jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin yan siyasa masu nagarta da aka taba samu daga arewacin Najeriya.

Ba zan taba sauya sheka zuwa PDP ba - El-Rufa'i

Amma, a martanin da ya yi, El-Rufai shima ta shafinsa na Twitter ya ce:

"Nagode @BwalaDaniel amma a'a, nagode. Ba za ta taba yiwuwa ba, ko gawa ta ba za a gani a harabar sabuwar jam'iyyar siyasar da ka shiga ba. Har yanzu ina dariya!!! - @elrufai".

Kakakin PDP Bwala: Muna Nan Daku, El-Rufai Zai Lallaba Ya Koma Jam’iyyar APC Nan Gaba

Tunda farko, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Bwala Daniel, ya yi hasashen abin da zai faru gabanin babban zaben 2023.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta, Daniel wanda ya fice daga jam’iyyar APC a baya-bayan nan ya ce gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna zai koma jam’iyyar PDP nan ba da jimawa ba.

Jigon na PDP ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan batutuwa El-Rufai na matsayin zamansa a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel