Gwamna El-Rufai ga Daniel Bwala: Ko Gawata Ba Za Ta Shiga PDP ba

Gwamna El-Rufai ga Daniel Bwala: Ko Gawata Ba Za Ta Shiga PDP ba

  • Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya sha alwashin ba zai taba shiga jam’iyyar adawa ta PDP ba kafin 2023
  • El-Rufai ya mayar da martani ne ga kakakin yakin neman zaben Atiku, Daniel Bawala, wanda ya bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnan Kaduna zai fice daga APC zuwa PDP
  • Gwamnan na Kaduna, ya ce ko gawarsa ba za ta koma jam’iyyar adawa ta PDP a wata makala da ya yada Twitter

Jihar Kaduna – Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi magana game da yuwuwar ya koma jam’iyyar PDP gabanin babban zabe na 2023.

Gwamnan na Kaduna ya mayar da martani ne ga ikirarin da kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Daniel Bawala, ya yi a shafinsa na Twitter.

A baya Bwala ya yi hasashen cewa, tsohon ministan na babban birnin tarayya (FCT) zai fice daga jam’iyyar APC mai mulki nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Sace Gwiwan Kakakin Atiku, Ya Ce Ko Gawarsa Ba Za A Tsinta Kusa Da PDP Ba

Martanin El-Rufai ga Daniel Bwala
Gwamna El-Rufai: Ko gawata ba za ta shiga PDP balle kuma da raina na bar APC | Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

A shafinsa na Twitter, Bwala wanda har a kwanan baya dan jam’iyyar APC ne ya ce yana da kwarin gwiwar cewa El-Rufai zai shigo PDP kafin zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana Gwamnan Kaduna a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan siyasar da Arewa ta taba yi a tarihi.

Ba zan taba komawa PDP ba – El-Rufai

Da yake mayar da martani ga hasashen Bwala, ta Mallam Nasiru El-Rufai ya ce sam da kamar wuya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta adawa.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

"Na gode @BwalaDaniel amma a'a, na gode. Har abada, ko gawata ba za a samu a kusa da sabuwar jam’iyyar ku ta siyasa ba. Har yanzu dai dariya nake!!! - @elrufai"

Kakakin PDP Bwala: Muna Nan Daku, El-Rufai Zai Lallaba Ya Koma Jam’iyyar APC Nan Gaba

Kara karanta wannan

Jigon PDP: Muna nan daku, El-Rufai zai lallaba ya koma jam'iyyar PDP nan da 2023

A wani labarin, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Bwala Daniel, ya yi hasashen abin da zai faru gabanin babban zaben 2023.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta, Daniel wanda ya fice daga jam’iyyar APC a baya-bayan nan ya ce gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna zai koma jam’iyyar PDP nan ba da jimawa ba.

Jigon na PDP ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan batutuwa El-Rufai na matsayin zamansa a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel