Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

  • Wole Soyinka ya yi maraba da batun tunbuke Muhammadu Buhari daga kan karagar mulkin kasar nan
  • Farfesa Soyinka yace kusan kowa ya gamsu da Shugaban Najeriyan ya gaza, har ta kai ana neman a tsige shi
  • Masanin ya bukaci a hada da Gwamnoni a tunbuke saboda rawar da suka taka a zaben tsaida gwanin APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A ranar Talata, 3 ga watan Agusta 2022, Farfesa Wole Soyinka ya nuna goyon bayansa ga yunkurin majalisa na tsige Muhammadu Buhari.

Jaridar Punch tace shahararren Farfesan wanda ya taba lashe kyautar Nobel laureate ta Duniya ya nuna goyon bayansa ne a Abeokuta, a jihar Ogun.

Da yake jawabi a bikin da aka yi domin murnar cikar Abeokuta Club shekara 50 a Duniya, Soyinka ya tabo batun tsige shugaba a tsarin farar hula.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sako karin mutum 5 daga fasinjojin jirgin kasa Abj-Kad da suka sace

Soyinka ya yi bayani a kan yadda ‘yan siyasa ke gabatar da kansu a zabe, su shiga takara bayan sun tallatawa talakawa manufofin da suke da shi.

Farfesan yace a wasu lokuta, ana karya alkawarin da aka yi wa al’umma, daga cikin yadda ake maganin wannan shi ne sai a tunbuke mai mulki.

Rashin tsaro a Najeriya

Masanin ya yi misali da halin da ake ciki a yanzu inda wasu ‘yan majalisa ke neman tunbuke shugaba (Muhammadu Buhari) saboda rashin tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Soyinka
Farfesa Wole Soyinka
Asali: Twitter

A ra'ayinsa, kowa ya yarda Buhari ya gaza, hakan ta sa ake neman a sauke shi.

PM News ta rahoto Soyinka yana maganar malamin da aka ji yana addu’a ‘yan bindiga su samu damar sace shugaban kasar, ayi garkuwa da shi.

Tsaida Tinubu takara

A cewar Soyinka, shugaba mai-ci ya sabawa ka’idar damukaradiyya tun da ya sa baki wajen fito da wanda zai gaje shi a kan mulki bayan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Mafi Yawan Sanatoci Sun Yi Na’am da Yunkurin Tunbuke Buhari Inji Sanatan Bauchi

Kowa yana da kuri’a daya ne a damukaradiyya, don haka Farfesan yake so a tsige har gwamnonin da suka marawa Bola Tinubu baya ya samu tikiti.

Babban Akantan nan, Gbenga Adeoye; da Ogo-Oluwa Bankole wanda ‘dan kasuwa ne da kuma Sunday Oduntan sun gabatar da jawabi a wajen taron.

An gudanar da jawabai ne a taron a kan taken shugabanci a tsarin damukaradiyya. Femi Falana da Ishaq Oloyede suna cikin wadanda suka halarta.

Obidients sun fusata

Kun ji labari wani rubutu da Sam Omatseye ya yi, ya fusata magoya bayan Obi, inda ya tona asirin wadanda ke tare da ‘dan takaran LP a zaben 2023.

Dama can Peter Obi yana da wasu magoya baya masu kiran kansu ‘Obidients’, wanda shi karan kansa yake faman shan wahala wajen shawo kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel