Daga Rubutu a Kan Peter Obi, Magoya-baya na Barazanar Kashe Ni inji Marubuci

Daga Rubutu a Kan Peter Obi, Magoya-baya na Barazanar Kashe Ni inji Marubuci

  • Kwararre kuma fitaccen marubucin nan, Sam Omatseye ya na fuskantar barazana a rayuwarsa
  • Mista Omatseye ya yi wani rubutu wanda ya yi kaca-kaca da Peter Obi a karshen makon jiya
  • Tun da ya yi wannan rubutu, magoya bayan ‘dan takaran shugaban kasar suka taso shi a gaba

Lagos - Shahararren ‘dan jaridar kasar nan, Sam Omatseye, ya koka game da barazanar da yake fuskanta a dalilin wani rubutu da yayi a makon jiya.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sam Omatseye ya tada kura musamman a shafukan sada zumunta tun bayan rubutun da ya yi wanda ya yi wa take da ‘Obi-tuary’.

Omatseye ya fito shafinsa na Twitter yana mai cewa magoya bayan ‘dan takarar jam’iyyar Labor Party, Peter Obi suna yi masa barazana har ga rayuwarsa.

“Mista Peter Obi, ka jawo hankalin magoya bayanka. Suna kira na, kuma suna yi mani barazanar kisa.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya yi Magana Yayin da Jita-jitar Tunbuke shi ke yin Karfi a Majalisa

Da zarar wani abin ya faru da ni, kai za a damke da laifi.” - Sam Omatsaye.

‘Obidients’ sun shahara a Twitter

‘Dan takaran na zaben 2023 yana da magoya baya masu dumin kirji a shafukan sada zumunta na zamani wadanda suke kiran kansu da ‘Obidients’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi
'Dan takaran LP, Peter Obi a Osun Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Omatseye ya samu kansa a matsala tun da rubutunsa na ‘Obi-tuary’ ya fito a wata jarida, yana caccakar ‘Obidients’ da gwaninsu mai neman mulki.

The Cable tace Omatseye ya bayyana takarar Obi a matsayin mafakar tsageru, yake cewa masu rajin kafa kasar Biyafara sun labe a karkashin inuwarsa.

Marubucin yake cewa daga cikin wadanda suke tunkaho da ‘dan takaran, har da masu ilmin da suka rika sukarsa a lokacin yana Gwamnan Anambra.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa magoya bayan tsohon gwamnan mai neman zama shugabancin kasa a 2023 sun yi wa kwararren marubucin rubdugu.

Kara karanta wannan

A jini na take: El-Rufai ya ce mutuwa ce kadai za ta raba shi jam'iyyar APC

Wasu suna zargin Mista Omatseye ya caccaki Obi ne saboda yana goyon bayan Bola Tinubu. Ba wannan ne karon farko da ya yi rubutunsa a kan 2023 ba.

Ku yi a hankali - Obi

A cikin watan da ya gabata ku ka samu labari cewa Peter Obi ya yi kira da babban murya ga magoya bayansa da su rika bin masu adawa da shi a hankali.

Ganin yadda wasu masoyansa suka yi wa Poju Oyemade kaca-kaca, ‘dan takaran yace a bukatar girmama ra’ayin kowa domin gamsar da masu kada kuri'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel