Jam'iyyar APC Ta Karbi Masu Sauya Sheka Sama da 2000 A Jihar Kebbi

Jam'iyyar APC Ta Karbi Masu Sauya Sheka Sama da 2000 A Jihar Kebbi

  • Jam'iyyar APC ta tarbi wasu jiga-jigan PDP da mambobi sama da 2,000 da suka sauya sheƙa a ƙaramar hukumar Shanga jihar Kebbi
  • Shugaban tawagar masu sauya sheƙan ya ce sun yanke koma wa APC ne saboda zahirin abin da suka gani a gwamnatin Bagudu
  • Manyan jiga-jigan APC a Kebbi da ya haɗa da kakakin majalisar dokoki, shugaban jam'iyya na jiha sun halarci tarɓan mutanen

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Kusan mutum 2,512 masu katin zama cikakkun mambobin jam'iyyar PDP a yankin ƙaramar hukumar Shanga, jihar Kebbi sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressive Congress APC a ƙarshen mako.

Vanguard ta ce tsohon shugaban PDP a ƙaramar hukumar, Alhaji Yakubu Dala, shi ya jagoranci mambobin zuwa APC tare da baki ɗaya shugabannin jam'iyyar da ke ci, Deleget, mata da shugabannin matasa.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Wurin taron sauya sheƙa a Kebbi.
Jam'iyyar APC Ta Karbi Masu Sauya Sheka Sama da 2000 A Jihar Kebbi Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dala ya alaƙanta dalilin shigar su APC da kyakkyawan jagoranci da yanayin tafiyar da mulkin gwamna Abubakar Atiku Bagudu da kuma danƙon haɗin kai da ke cikin jam'iyyar reshen jihar Kebbi.

A kalamansa ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kafin yanzu ni mamban PDP ne, amma yanzu na koma APC, zan iya cewa PDP ta mutu murus a Shanga, kuma sanadin sauya sheƙar mu jam'iyyar zata cigaba da tarwatsewa.

Mun zama yan uwan juna

Da yake maraba da masu sauya sheƙan, shugaban APC a Kebbi, Alhaji Muhammad Kana Zuru, ya tabbatar musu da cewa sun zama ɗaya da kowa a cikin jam'iyya.

Ya kuma tuna wa mazauna Shanga wasu daga cikin cigaban da gwamnatin Bagudu ta kawo yankin su, ya kuma roki su ƙara goyon bayan gwamnatin.

Kakakin majalisar dokokin Kebbi, Sani Abubakar Lolo, da SSG, Babale Umar Yauri, sun yi magana a wurin kan buƙatar mambobin jam'iyya su ƙara haɗa kansu don samar da cigaba ga mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Shugabannin NNPP Da Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheƙa Zuwa LP A Jiha Ɗaya Ta Arewa

A wani labarin kuma Babbar matsala sabuwa ta kunno, Wasu Sanatocin APC sun goyi bayan tsige shugaba Buhari

Elisha Abbo mai wakiltar mazaɓar Adamawa ta arewa, Sanata Elisha Abbo, ya goyi bayan a tsige shugaba Buhari.

A wani taron mambobin APC kiristoci da ya gudana a Abuja, Sanatan ya bayyana cewa Buhari ya gaza sauke babban nauyin dake kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel