Jam'iyyar LP Ta Karbi Daruruwan Masu Sauya Sheka Daga NNPP Da APC a Adamawa

Jam'iyyar LP Ta Karbi Daruruwan Masu Sauya Sheka Daga NNPP Da APC a Adamawa

  • Peter Obi ya samu ƙarin goyon baya yayin da ɗaruruwan mambobin NNPP da APC suka sauya sheka zuwa LP a jihar Aadamawa
  • Shugabannin jam'iyyar NNPP a matakin gundumomi biyar a ƙaramar hukumar Yola ta kudu ne suka jagoranci masu sauya sheƙan
  • Ɗan takarar gwamna karkashin LP yace tarihi na gab da sake maimaita kansa a Adamawa da ƙasa baki ɗaya

Adamawa - Jam'iyyar Labour Party (LP) ta karɓi aƙalla mutum 700 waɗan da suka sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP mai kayan marmari da APC a yankin ƙaramar hukumar Yola ta Kudu, jihar Adamawa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugabannin NNPP na gudumomi biyar a yankin ƙaramar hukumar ne suka jagoranci ɗaruruwan masu sauya sheƙan.

Tambarin jam'iyyar LP.
Jam'iyyar LP Ta Karbi Daruruwan Masu Sauya Sheka Daga NNPP Da APC a Adamawa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗan takarar gwamnan Adamawa ƙarƙashin inuwar LP, Umar Madawaki, da shugaban jam'iyya reshen jiha, Nicholas Christopher, da sauran shuwagabanni ne suka karɓi masu sauya sheƙar ranar Asabar a Yola.

Kara karanta wannan

Wani babban Jigon APC ya sauya sheƙa, Gwamna da wasu jiga-jigai sun tarbe shi zuwa PDP

Madawaki, mai rike da tikitin takarar gwamna na LP, ya ce masu sauya sheƙar sun yanke shawari mai kyau duba da karɓuwar da jam'iyyar Labour Party ta samu a sassan jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tarihi zai maimaita kansa

Ɗan takaran, wanda ya kafa misali da yadda jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP mai mulki ta kafa gwamnati a jihar, ya ce:

"Tarihi na gab da sake maimaita kansa a jihar Adamawa da Najeriya baki ɗaya, saboda jam'iyyar LP wata guguwace da ta shirya kawar da jam'iyyar All Progressive Congress watau APC a matakin ƙasa."
"Haka nan kuma LP ta shirya kawar da jam'iyyar PDP a matakin jiha daga bisani ta yi ɗare-ɗare kan madafun iko domin amfanin kowane ɗan Najeriya."

A wani labarin na daban kuma Gwamna Umahi Na Jihar Ebonyi Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani da Aka Canza

Kara karanta wannan

2023: 'Zan Kawo Karshen Yan Bindiga A Zamfara' Atiku Ya Karɓi Jiga-Jigan APC Da Suka Koma PDP

Gwamnan jihar Ebonyi ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar sanata mai wakiltar mazaɓar kudancin Ebonyi karkashin inuwar APC.

Magoya bayan APC sun halarci zaɓen wanda ya gudana a hedkwatar ƙaramar hukumar Afikpo ta arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel