Sanatan Jam'iyyar APC Ya Goyi Bayan A Tsige Shugaban Kasa Buhari

Sanatan Jam'iyyar APC Ya Goyi Bayan A Tsige Shugaban Kasa Buhari

  • Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazaɓar Adamawa ta arewa, Sanata Elisha Abbo, ya goyi bayan a tsige shugaba Buhari
  • A wnai taron mambobin APC kiristoci da ya gudana a Abuja, Sanatan ya bayyana cewa Buhari ya gaza sauke babban nauyin dake kansa
  • Mambobin majalisar dattawa sun fara yunkurin tsige Buhari ne yayin da ƙalubalen tsaro ta kara lalacewa

Abuja - Sanatan jam'iyyar APC, Elisha Abbo ya goyi bayan yunkurin takwarorinsa na tsagin adawa game da tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari,

Premium Times ta rahoto cewa Abbo, Mai wakiltar mazabar Adamawa ta kudu a majalisar dattawaan Najeriya, ya ce shugaban kasan ya gaza sauke nauyin da ke kansa na tsare rayukan al'umma.

Sanata Elissha Abbo.
Sanatan Jam'iyyar APC Ya Goyi Bayan A Tsige Shugaban Kasa Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanatan yayi wannan tsokaci ne a wurin taron jagororin APC mabiya adɗinin kirista da ya gudana a Abuja, inda wasu fitattun mambobin APC suka yi fatali da takarar musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari

Kalaman Abbo na zuwa ne awanni 48 bayan Sanatocin tsagin adawa mafi yawan su mambobin PDP sun yi barazanar tsige shugaban idan ya gaza shawo kan matsalar tsaro cikin wa'adin da suka dibar masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Snaatan ya goyi baya?

Dayake hira da Channel Tv, Sanata Abbo, ya ce yana goyon bayan lamarin ɗari bisa ɗari saboda shugaba Buhari, "Ya gaza sauke muhimmin nauyi na kare rayuka da dukiyoyin al'umma."

Tun da farko, Sanatan jihar Kogi, Smart Adeyemi, Wanda shi ma mamban jam'iyyar APC ne, ya bayyana cewa shirin tsige shugaban ƙasa wani mataki ne da kusan kowa ya yi na'am da shi a majalisar.

"Mataki ne da kowa ya yi na'am da shi domin Sanatoci huɗu ne kacal suke ɗan ja kan lamarin," inji shi yayin zantawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro : Mutum Na Farko Da Ya Soma Gabatar da Kudurin Tsige Buhari Dan APC ne - Shekarau

Yan Majalisun sun fara yunkurin tsige shugban ƙasaBuhari ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ta ƙara muni a sassan Najeriya da kuma barazanar kai hari babban birnin tarayya Abuja.

A wani labarin kuma Babban Sanatan APC Ya Bayyana Abubuwa 2 Da Za Su Hana Tsige Buhari

Jigo a jam'iyyar APC ya tofa albarkacin bakinsa kan yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari da yan majalisa ke yi.

A wani hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, Sanata Adeseye Ogunleye ya bayyana cewa addini da kabilanci za su hana a tsige Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel