Na Kusa Da Gwamna Tambuwal Da Kansiloli Takwas Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Na Kusa Da Gwamna Tambuwal Da Kansiloli Takwas Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

  • Makusancin Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban karamar hukumar Tangaza, Isah Bashar Kalanjine, ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Makusancin Gwamna Tambuwal din ya kara da yin tsarabar kansilolin karamar hukumarsa takwas zuwa jam'iyya mai mulkin kasar nan
  • Aliyu Wamakko ya karbe su hannu bibbiyu inda ya tabbatar da cewa za a yi tafiyar tare dasu wurin tabbatar da cigaban jam'iyyar da jihar baki daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Shugaban karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto kuma makusancin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Honarabul Isah Salihu Bashar Kalanjine, tare da kansiloli takwas na karamar hukumar duk a karkashin jam'iyyar PDP, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Jaridar Vanguard ta ruwairo cewa, kamar yadda takardar tace, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, jigon jam'iyyar na jihar kuma 'dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2023, ya karba masu sauya shekar a Gawon Nama dake jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Mayar da Kiristan Arewa saniyar ware: Babachir da Yakubu Dogara Sun Kai Wa Wike Ziyara A Jihar Ribas

Gwamna Tambuwal
Na Kusa Da Gwamna Tambuwal Da Kansiloli Takwas Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC. Htot daga premiumtimes.ng
Asali: UGC

Sunayen kansilolin dake kan kujerar su ta mulki da suka sauya sheka sun hada da Honarabul Zakariyya Madugu, wanda 'dan takara ne a jam'iyyar PDP a zaben fidda gwanin da aka yi kwanan nan.

Sauran sun hada da Honarabul Abubakar Abubakar Kalanjine, Honarabul Abubakar Aliyu, Honarabul Halilu Aliyu, Honarabul Ibrahim Sarkin Tudu da Honarabul Musa Sulaiman Sakkwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran kansilolin biyu sun hada da Honarabul Abdullahi Garba da Honarabul Jamilu Muhammad.

A yayin karbarsu tare da musu maraba, Sanata Wamakko ya tabbatar musu da cewa za a tafi tare da su wurin ganin cigaban jam'iyyar da jihar baki daya, Premium Times ta rahoto hakan.

Ya bayyana tabbacinsa na cewa, jam'iyyar APC zata kwashe dukkan kujerun 'yan takara a zaben 2023 mai zuwa.

A wani labarin kuma Wani babban Jigon APC ya sauya sheƙa, Gwamna Tambuwal da wasu jiga-jigai sun tarbe shi zuwa PDP

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Nada El-Rufai Da Oshiomhole Manyan Mukamai A Kungiyar Kamfen Dinsa

Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal ya karbi wani babban jigon APC a jihar da ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP.

Ɗahiru Yabo wanda ya samu kyayyawan maraba, ya ce ba zai iya zama cikin tawagar da ba ta da demokaraɗiyya a cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel