Tsohon Kwamishinan Kuɗi Kuma Na Hannun Daman Ministan Buhari Ya Fice Daga APC

Tsohon Kwamishinan Kuɗi Kuma Na Hannun Daman Ministan Buhari Ya Fice Daga APC

  • Tsugune ba ta kare ba a jam'iyyar APC mai mulki, na hannun daman ministan cikin gida ya sauya sheka zuwa PDP a Osun
  • Wale Bolorunduro, tsohon kwamishinan kuɗi a jihar Osun ya ce sai da ya ji ta bakin masoya da iyalansa kafin yanke hukunci
  • Jam'iyyar APC ta tsinci kanta cikin rikici tun bayan kammala zaɓen fidda gwani wanda har yanzun yake kwashe mambobinta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Dakta Wale Bolorunduro, wanɗa ya rike kwamishinan kuɗi zamanin mulkin tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola, ya sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDP.

Punch ta rahoto cewa Bolorunduro, na hannun daman Aregbesola, ba ya ga maciji da gwamna Gboyega Oyetola, musamman game da ciyo ba shi da kuma lokacin da gwamnati ta yanke bin kwakkwafi kan makarantun tsohon gwamna ya gina.

Siyasar Najeriya.
Tsohon Kwamishinan Kuɗi Kuma Na Hannun Daman Ministan Buhari Ya Fice Daga APC Hoto: Hon Asp Seyi
Asali: Facebook

Da yake jawabi ga manema labarai a Osogbo, inda ya sanar da duniya ya fice daga jam'iyyar APC, Bolorunduro, ya ce gwamnatin jihar da ke ci yanzu ta zarce tunani wajen yaudara, rashin adalci da sanin ya kamata.

Kara karanta wannan

Ban ji dadi ba: Ganduje ya bayyana matakin da zai dauka kan yajij aikin ASUU

Tsohon kwamishinan ya ce shugabancin APC a jihar Osun ya watsar da shi gefe ta yadda har abubuwan da ke faruwa a gundumarsa ma ba'a sanya shi a ciki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa sai yanzu ya bar APC?

A cewarsa, matakin da ya ɗauka na barin APC ba don siyasarsa bane, inda ya ƙara da cewa bayan tattauna wa da masoyansa da iyalansa, an cimma matsayar ya matsa zuwa PDP.

A rahoton Premium Times, Bolorunduro ya ce:

"Na kasance a APC na shekara Takwas ba tare da ta taimake ni ko ta amfane ni ko an bani wani muƙami ba, haka na mata aiki a zaɓukan 2015 da kuma 2019, zan iya gudanar da rayuwa ba'a cikin gwamnati ba."
"Na tattauna da magoya baya, masoya, abokai da iyalai na, waɗan da ke ganin ya dace mu koma PDP kuma mu yi aiki da ita don haskaka jahar Osun."

Kara karanta wannan

Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

A wani labarin kuma kun ji cewa Tsofaffin Mataimakan Gwamna Biyu Da Dubbannin Mambobin APC Sun Koma PDP

Tsofaffin mataimakan gwamna 2 a Kebbi da wasu shugabannin APC sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP.

Haka a jihar Bauchi, dubbannin mambobin APC mata sun ce gwamnati ta ba su kunya, sun koma PDP don su tallafi Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel