Tsofaffin Mataimakan Gwamna Biyu Da Dubbannin Mambobin APC Sun Koma PDP

Tsofaffin Mataimakan Gwamna Biyu Da Dubbannin Mambobin APC Sun Koma PDP

  • Tsofaffin mataimakan gwamna 2 a Kebbi da wasu shugabannin APC sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
  • Haka a jihar Bauchi, dubbannin mambobin APC mata sun ce gwamnati ta ba su kunya, sun koma PDP don su tallafi Atiku
  • Kowace jam'iyyar siyasa na Najeriya na cigaba da kokarin shirya wa domin tunkarar babban zaɓen 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Tsoffin mataimakan gwamna biyu a jihar Kebbi, Ibrahim K. Aliyu da Mohammed Bello Dantani, sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa PDP

Leadership ta ruwaito cewa mutanen biyu sun sauya sheƙan ne tare da mataimakin shugaban APC na shiyya, Alhaji Atiku Alaramma Warrah, Sakataren tsare-tsare na jiha, Abdullahi Mai Unguwa, da wasu 43 zuwa PDP.

Siyasar Najeriya.
Tsofaffin Mataimakan Gwamna Biyu Da Dubbannin Mambobin APC Sun Koma PDP Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Yayin da suke tabbatar da mubaya'ar su a Sakatariyar PDP da ke Birnin Kebbi, jiya Laraba, Aliyu da Kabi, sun ce sun yanke barin APC ne saboda nuna wariya da gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da muhimman ayyuka.

Kara karanta wannan

Gwamnoni arewa uku da wasu jiga-jigan APC sun sa labule da Tinubu, Shettima a Abuja

A jawabin su, "Gwamnati ta yi alƙwarin ba mu muƙami a lokacin zaɓen fidda gwani amma sai muka ƙare da babu. Sun san ba zasu kai labari ba a 2023 domin mambobin su sun rasa kwarin guiwa a jam'iyyar."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba zamu nuna muku banbanci ba - PDP

Shugaban PDP a jihar Kebbi, Alhaji Bello Suru, wanda sakatarensa ya wakilce shi, ya musu maraba da zuwa jam'iyyar tare da tabbatar musu da cewa an zama ɗaya, musamman idan suka kafa gwamnati a 2023.

Ya ƙara da tabbatar wa masu sauya sheƙan cewa jam'iyyar PDP zata canza yanayin tafiyar da gwamnati idan mulki ya dawo hannun ta.

Matan APC sama da 5,000 sun koma PDP a Bauchi

A jihar Bauchi, matan jam'iyyar APC sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP karkashin jagorancin Fatima Muhammed.

Kara karanta wannan

Mambobi 20,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a jiha ɗaya, Shugabar mata ta rungume su hannu biyu

Da take zantawa da manema labarai, Fatima ta ce sun ɗauki wannan matakin ne saboda gazawar gwamnatin APC a matakin kasa wajen cika alƙawarin tsamo yan Najeriya daga bakin talauci, yunwa da sauran su.

Ta ce masu sauya sheƙa 5,000 zasu yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, gwamna Bala Muhammed, da sauran yan takarar PDP a zaɓen 2023.

A wani labarin kuma Mambobin APC da PDP 200 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar LP a Abuja

Jam'iyyar Labour Party (LP), ranar Litinin, ta karɓi masu sauya sheƙa sama da 200 daga manyan jam'iyyun siyasa PDP da APC a gundumar Gaube, ƙaramar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja.

Daily Nigerian a rahoton ta tace masu sauya sheƙan, waɗan da suka miƙa tsintsiyoyi, laima, katin jam'iyya da fastoci, sun ce matakin ya zama wajibi a kansu domin Demokaraɗiyya ta gaske ta farfaɗo a kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aike da muhimmin saƙo ga shugaban jam'iyyar APC na ƙasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel