Dole za mu shiga lamarin nan: Ganduje ya koka kan ci gaba da yajin aikin ASUU

Dole za mu shiga lamarin nan: Ganduje ya koka kan ci gaba da yajin aikin ASUU

  • Gwamnan jihar Kano ya taya 'yan kungiyar kwadago da ASUU nuna rashin jin dadinsu ga yadda ASUU ke yajin aiki
  • Gwamnatin tarayya ta gaza biya wa kungiyar ASUU bukatunta na kudaden albashi da alawus-alawus
  • Gwamna Ganduje ya ce gwamnonin Najeriya za su sa baki domin ganin an dinke barakar da ke tsakani

Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar Talata, ya tabbatar wa kungiyar kwadago ta Najeriya cewa kungiyar gwamnonin Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya a jihar, wadanda suka je gidan gwamnati, inda suka yi zanga-zangar nuna goyon bayansu ga ASUU, rahoton Punch

Kara karanta wannan

Dillalan jakuna: 'Yan Najeriya miliyan 3 za su rasa sana'a idan aka hana yanka jakuna

Ganduje ya ce zai tsoma baki a yajin aikin ASUU
Dole zan shiga lamarin nan: Ganduje ya koka kan yajin aikin ASUU | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gwamnan wanda ya koka da rikicin da aka dade ana yi ya ce, kungiyar gwamnoni za ta gana da Gwamnatin Tarayya ta fannin shawarwari domin warware rikicin da nufin ceto tsarin ilimin kasar.

A cewar Ganduje:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Za mu yi galaba a kan Gwamnatin Tarayya ta fannin shawarwari domin dole ne a magance rikicin nan domin a ceto tsarin.
"Dole ne a warware wannan rikicin don taimakawa wajen ceto tsarin. Ba ma son rugujewar tsari a kasar nan kwata-kwata.”

Ya lura cewa malaman jami'o'in da suke yajin aikin "suna cikin yajin aikin ne don ceto tsarin daga rugujewa."

Yayin da yake kokawa kan halin da daliban kasar nan suke ciki na zaman banza na tsawon lokacin, ya bayyana cewa:

“Ni da abokan aikina daga dukkan jihohin kasar nan 36, ba tare da la’akari da bambance-bambancen jam’iyyarmu ba, mun damu da tsawaitar yajin aikin nan, kuma za mu hada kawunanmu domin kawo karshen rikicin."

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

Gwamnan ya yabawa ’yan kwadago da dalibai da sauran wadanda suka halarci zanga-zangar bisa nuna kokarinsu da kuma daukar nauyin gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Ganduje ya kuma yi alkawarin mika wasikar da ya karba daga shugabannin kwadago zuwa ga ministan ilimi, Adamu Adamu, domin mikawa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

NLC ta yaba Ganduje

Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban kungiyar NLC reshen Kano, Kabiru Minjibir, ya ce zanga-zangar na bin umarnin hedikwatar kungiyar ta kasa ne na tilastawa gwamnati yin abin da ya dace.

Ya kuma yabawa Ganduje kan rashin daukar wasu abokan aikinsa na hana malaman jami'o'i albashi saboda suna cikin yajin aiki.

A cewar Kwamared Minjibir:

“A gaskiya muna godiya ga gwamnatin jiha karkashin jagorancin ka, gwamnan jama’a, Dakta Abdullahi Ganduje, bisa ga wannan gagarumin mataki da ka dauka na rashin hana albashin malaman jami’o’in jihar.
"Wannan ya nuna kai gwamna ne mai son ilimi."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ma'aikatan wutar lantarki za su mamaye Najeriya domin taya ASUU zanga-zangar nuna fushi

Daga cikin wadanda suka halarci zanga-zangar ta lumana akwai ‘yan kungiyar ASUU, kungiyoyin dalibai, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin matasa da masu rajin kare hakkin bil’adama da dai sauransu.

Ma'aikatan wutar lantarki sun bi sahu, za su taya ASUU zanga-zanga

A wani labarin, Punch ta ruwaito cewa, ma’aikatan wutar lantarki a karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), sun ce za su bi sahun kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a zanga-zangar hadin gwiwa da ta shirya yi kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Kungiyar kwadago ta NLC ta umarci ma’aikata da su fito zanga-zanga a fadin kasar nan a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin nuna goyon bayansu ga yajin aikin da ASUU ta shiga.

Ma'aikatan jiragen sama, ma'aikatan inshora da ma'aikatan kudi, da sauransu su ma sun yi alkawarin shiga zanga-zangar, rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel