2023: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A PDP Ya Fadi Alheri Kan Tinubu, Ya Aika Masa Rubutu Mai Ratsa Zuciya

2023: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A PDP Ya Fadi Alheri Kan Tinubu, Ya Aika Masa Rubutu Mai Ratsa Zuciya

  • Dele Momodu, jigo a jam'iyyar PDP, ya ce karfin hali da jarumtar Tinubu ne dalilin da yasa ya samu nasarori da dama a rayuwarsa
  • A sakon taya Tinubu murna, tsohon mai neman takarar shugaban kasar na jam'iyyar adawa ya ce Allah na son Tinubu sosai
  • Bugu da kari, Momodu ya ce mutum kamar Tinubu, wanda ya sha gwagwarmaya sosai ba fa kaman kowa ya ke ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon mai neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi rubutu mai ratsa zuciya don taya Asiwaju Bola Tinubu murna bisa karfin halinsa.

A rubutun da wani daga cikin magoya bayan Tinubu, Imran Muhammad, ya gani, Momodu ya ce dan takarar na shugaban kasa na jam'iyyar APC yana da karfin hali da juriya, duba da irin gwagwarmayar da ya yi a rayuwa.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'

Momodu da Tinubu.
2023: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A PDP Ya Yabi Tinubu, Ya Aika Masa Rubutu Mai Ratsa Zuciya. Hoto: @imranmuhdz.
Asali: Twitter

Mawallafin Mujallar Ovation ya ce tabbas Allah na son Tinubu hakan yasa ya bashi ikon yin nasara a gwagwarmayar da ya yi a rayuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga abin da sakon ya ce:

"Tinubu yana da jarumta ba irin ta kowa ba. Na yi imanin cewa jarumtarsa ce ta kai shi matsayin da bai taba tunani ba.
"Mutum irin sa wanda ya yi gwagwarmaya ya yi nasara ba mutum bane kaman kowa. Tabbas Allah na kaunarsa sosai. Ya yi yaki da dama ya kuma yi nasara."

An kuma wallafa irin wannan rubutun a shafin Joe Igbokwe, daya daga cikin na hannun daman Tinubu a shafinsa na Facebook a ranar Talata 26 ga watan Yuli.

2023: Tinubu Ya Nada El-Rufai Da Oshiomhole Manyan Mukamai A Kungiyar Kamfen Dinsa

A wan rahoton daban kun ji cewa an zabi Mallam Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna da Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Jihar Edo domin jagorantar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

An nada Adams Oshiomhole a matsayin ciyaman na kungiyar kamfen din Bola Tinubu, yayin da Nasir El-Rufai aka na shi direkta janar na kungiyar yakin neman zaben.

Shafin kungiyar kafar watsa labarai masu goyon bayan Tinubu, TMS, ce ta sanar da nadin a shafinta na Twitter @TinubuMediaS kamar yadda Legit Hausa ta gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164