2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'

2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'

  • Babban jam'iyyar hammaya a Najeriya ta PDP ta bukaci Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa na APC ya janye takararsa
  • Debo Ologunagba, sakataren watsa labarai na kasa na PDP ne ya yi wannan kirar yana mai cewa zargin da ake yi wa Tinubu na dako hayar makanikai da wasu a matsayin Bishop wurin kaddamar da Shettima ya nuna ba shi da gaskiya
  • Ologunagba ya yi ikirarin cewa yan Najeriya sun yi tir da abin da ya kira yaudara da Tinubu ya yi a wani yunkuri na nuna cewa kiristoci na tare da shi

Jam'iyyar PDP ta bukaci dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, nan take ya janye takararsa saboda ikirarin cewa ya dako hayar 'Bishop Bishop' na bogi su hallarci kaddamar da mataimakinsa, Kashim Shettima, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Atiku: Sowore Bai San Komai Ba Game Da Najeriya

Tambarin PDP
2023: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Kan 'Fastocin Bogi'. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma'a, sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce Tinubu da APC sun aikata babban laifi kuma tare da yaudara, ya kara da cewa ba su cancanta shiga zaben ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jam'iyyar PDP, da murya mai karfi ta yi tir da abin rashin da'a da tsokana da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya aikata," in ji shi.

Ya ce yan Najeriya sun yi damu matuka bisa hotuna da bidiyon makanikai da yaran mota da yan damfara da aka sani sanye da kayan Bishop na karya da aka dauko haya wurin kaddamar da Sanata Kashim Shettima, mataimakin Asiwaju Bola Tinubu, wanda mutane da dama suka ki amincewa da shi.

Ya ce dan takarar na jam'iyyar APC ya rasa hali na gaskiya da ake bukata daga shugaba don haka kada ya bata lokacinsa ya yi takarar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku ya bayyana matsayarsa ta yin sulhu da gwamnan PDP Wike

Kaddamar Da Shettima: Hotunan Yadda Matasan Najeriya Suke Zolayar APC Da Gasar #BishopChalllenge a Tuwita

A wani rahoton, wasa matasan Najeriya sun fara wani gasa da suka yi wa lakabi da #BishopChallenge domin zolayar jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Hotuna da bidiyon Bishop Bishop da fastoci a wurin taron kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima, a ranar Laraba 20 ga watan Yuli ne suka janyo gasar.

Tunda farko, hotunan fastocin a taron da APC ta yi a birnin tarayya Abuja, ya janyo cece-kuce tsakanin wasu yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel