Atiku Abubakar: Sowore Bai San Komai Ba Game Da Najeriya

Atiku Abubakar: Sowore Bai San Komai Ba Game Da Najeriya

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben shekarar 2023 ya ce Omoyele Sowore dan takarar AAC bai san komai ba game da Najeriya
  • Atiku ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya kan sukar da Sowore ya masa na cewa yana mataimakin shugaban kasa Obasanjo ya kashe $16bn kan lantarki kuma har yau wutar bata zauna ba
  • Turakin na Adamawa ya yi bayanin cewa sun kashe kudin wurin gina tashoshin samar da lantarki guda 9 kuma lantarkin da ake samarwa ya karu sai dai rabawa ne matsala amma Sowore ba zai sani ba tunda ba zama ya ke a kasar ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC), bai san komai ba game da Najeriya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku ya bayyana matsayarsa ta yin sulhu da gwamnan PDP Wike

Atiku, a ranar Laraba, yayin martani kan kaddamar da kamfanin man fetur na kasa, (NNPC Limited), ya rubuta a Twitter a 2018 cewa zai sauya wa NNPC tsari amma gwamnatin APC ta soki abin.

Atiku Abubakar.
Sowore Bai San Komai Ba Game Da Najeriya, In Ji Atiku Abubakar. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"A 2018 na bayyana cewa zan sauya tsarin NNPC don inganta riba da ayyuka. Gwamnatin APC ta soke ni saboda hangen nesa na.
"Amma yau, na yi murnan ganin gwamnatin ta dauki matakin yin abin da na bada shawara. Mataki ne mai kyau duk da cewa akwai sauran aiki.
"Ina fatan zan samu damar karasa aikin in sauya NNPC zuwa kamfani irin na kasashen duniya kamar NLBG, Aramco na Saudiyya da Petrobras na Brazil inda yan Najeriya da kamfanonin Najeriya za su saka hannun jari."

A martanin da ya yi kan rubutun, Sowore ya soki tsohon mataimakin shugaban kasar saboda kokawa da ya yi game da dauke wuta a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

Sowore ya ce Atiku ne mataimakin shugaban kasa a lokacin da mai gidansa ya ware Dallar Amurka Biliyan 16 don farfado da lantarki amma ba wani abin azo a gani.

Sowore bai san komai kan Najeriya ba, Atiku

Da aka tambayi Atiku game da lamarin yayin hira a Arise TV a ranar Juma'a, ya ce dan takarar shugaban kasar na AAC baya zama a Najeriya kuma yana zuwa ne bayan kowanne shekara hudu don yin takarar zabe.

Ya ce:

"Eh, abokin hammaya na ne, me ka ke tsammanin zai ce? Dama ba a Najeriya ya ke zama ba. Bai san yadda aka aiwatar da tsarin ko kirkirarta ba. Da muka zo, megawatt 2000 ake samarwa. Mun fara gina tashoshin samar da lantarki, lokacin da muka gama guda tara, lantarkin da ake samarwa ya tashi daga 2000 zuwa 13,000 megawatt.
"Jonathan ya karasa gine tashohin wutar. Umaru Yaradua yana aiki kansu. Ya rasu kuma Jonathan ya cigaba ya karasa. Shi yasa aka samu karin wuta da ake samarwa amma akwai matsalar rabarwa, za a samu matsala.

Kara karanta wannan

Lantarki: ‘Yan Takaran Shugaban kasan 2023, Atiku, Obi da Sowore sun yi Karo

"Shi (Sowore) bai ma sani ba, saboda baya zama a kasar. Ya kan zo ne duk bayan shekaru hudu ya yi takarar shugaban kasa ya koma. Zai fadi ya koma ya sake dawowa. Don haka, mai Sowore ya sani game da kasar nan? Ba abin da ya sani, bai san komai ba."

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce bai taba zama fiye da wata guda ba a Dubai ba bayan lokacin da ya karatun digirinsa na biyu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya bayyana hakan ne a yayin hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel