Zaben 2023: Jerin Sanatoci 44 da ba za su Dawo Majalisa ba Bayan 2023
Akalla sanatoci 44 ne ba za su dawo majalisa ba bayan zaben 2023 saboda wasu dalilai na cikin gida a jam'iyya ko siyasar yanki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Da yawa daga cikin Sanatocin da ba za su dawon ba sun fito ne daga jam'iyyun PDP da na APC mai mulki.
Bincike ya nuna cewa, da yawa daga cikin Sanatocin sun sha kaye ne a zaben fidda gwani, wasu kuma bayan sun sha kaye, sun sauya sheka zuwa jam’iyyu daban-daban domin samun tikitin tsayawa takara.
‘Yan takaran da suka fito daga zaben fidda gwanin wasu jam’iyyu daban-daban ne kadan hukumar zabe ta INEC ta amince da su.
Jerin Sanatocin da ba za su koma zauren Majalisar Dattawa ba
- Ahmad Lawan
- Ibikunle Amosun (Ogun ta tsakiya)
- Ajayi Boroffice (Ondo ta arewa)
- Rochas Okorocha (Imo ta yamma)
- Ovie Omo-Agege
- Sanata Emmanuel Bwacha daga Taraba
- Sanata Uba San (Kaduna ta tsakiya)
- Aishatu Dahiru daga Adamawa
- Teslim Folarin (Oyo ta arewa)
- Sandy Onor (Cross River ta tsakiya)
- Nora Daduut (Plateau ta Kudu)
- Theodore Orji (Abia ta tsakiya)
- Oluremi Tinubu (Legas ta tsakiya)
- Dimka Hezekiah (Plateau ta tsakiya)
- Gyang Istifanus (Plateau ta Arewa)
- Smart Adeyemi (Kogi ta yamma)
- Yakubu Oseni (Kogi ta tsakoya)
- Sabi Abdullahi (Niger ta arewa)
- Godiya Akwashiki (Nasarawa ta arewa)
- Ibrahim Oloriegbe (Kwara ta arewa)
- Orker-Jev Emmanuel (Benue ta arewa maso yamma)
- Yusuf Yusuf (Taraba ta tsakiya)
- Amos Bulus (Gombe ta Kudu)
- Ayo Akinyelure (Ondo ta tsakiya)
- Nicholas Tofowomo (Ondo ta Kudu)
- Tolu Odebiyi (Ogun ta yamma)
- Matthew Urhoghide (Edo ta Kudu)
- Gershom Bassey (Cross Rivers ta Kudu)
- James Manager (Delta ta Kudu)
- George Sekibo (Rivers ta Gabas)
- Betty Apiafi (Rivers ta yamma)
- Albert Bassey (Akwa Ibom ta arewa maso gabas)
- Chris Ekpenyong (Akwa Ibom ta arewa maso yamma)
- Rochas Okorocha (Imo ta yamma)
- Hadejia Ibrahim (Jigawa ta arewa maso gabas)
- Sankara Abubakar (Jigawa ta arewa maso yamma)
- Mohammed Nakudu (Jigawa Kudu maso Yamma)
- Bello Mandiya (Katsina ta Kudu)
- Barkiya Kabir (Katsina ta arewa)
- Lawali Anka (Zamfara ta Yamma)
- Danjumah La’ah (Kaduna ta kudu)
- Moses Cleopas (Bayelsa ta tsakiya)
- Mohammed Bulkachuwa (Bauchi ta arewa)
- Chukwuka Utazi (Enugu ta arewa)
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rikicin kujerar Sanata Ahmad Lawan, ya dauki zafi, Machina ya yi wa Shugaban APC raddi
A wani labarin, Hon. Bashir Sheriff Machina ya fito ya yi martani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu a kan wasu kalamai da ya yi.
Da yake zantawa da BBC Hausa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni 2022, Bashir Sheriff Machina ya yi Allah-wadai da irin maganganun Abdullahi Adamu.
Kamar yadda ya fada, ‘dan takaran na Sanatan Yobe ta Arewa ya ce yana neman hakkinsa ne a APC, domin bai fada da Sanata Ahmad Lawan ko wani.
Asali: Legit.ng