Rikicin kujerar Sanata Ahmad Lawan, ya dauki zafi, Machina ya yi wa Shugaban APC raddi

Rikicin kujerar Sanata Ahmad Lawan, ya dauki zafi, Machina ya yi wa Shugaban APC raddi

  • Bashir Sheriff Machina ya sake maida martani bayan hirar da aka yi da Sanata Abdullahi Adamu
  • An ji shugaban na Jam’iyyar APC yana kare matsayar APC na mikawa INEC sunan Ahmad Lawan
  • Hon. Machina ya karyata shugaban APC na kasa, ya ce sam Lawan bai nemi takara a jihar Yobe ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe – Hon. Bashir Sheriff Machina ya fito ya yi martani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu a kan wasu kalamai da ya yi.

Da yake zantawa da BBC Hausa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni 2022, Bashir Sheriff Machina ya yi Allah-wadai da irin maganganun Abdullahi Adamu.

Kamar yadda ya fada, ‘dan takaran na Sanatan Yobe ta Arewa ya ce yana neman hakkinsa ne a APC, domin bai fada da Sanata Ahmad Lawan ko wani.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi wa Obasanjo shagube, yace ba zai nemi ya sake zarcewa a mulki ba

Machina ya fadawa BBC cewa bai dace dattijo irin Sanata Abdullahi Adamu ya rika fadar maganganu masu zafi a kan shi ba, a lokacin shirin zabe.

Kalamansa ba su dace ba

“Dattijo bai kamata ya yi magana irin wannan a daidai wannan lokaci ba. Idan aka sako zabe a gaba, ba a yin kalmomi masu zafi ko batanci ko barazana ga mai neman ‘yancinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba laifi ba ne, damukaradiyya ake yi, mu ba fada mu ke yi da Ahmad Lawan ko wani ba. Ba mu fada da kowa." - Bashir Machina.
Shugaban APC
Shugaban APC, Abdullahi Adamu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Mun tsaya a matsayinmu na masu neman hakkinmu. Bai dace babban mutum ya fito karara, yana irin wannan kalma ba."

‘Dan siyasar yace su na gudun shugaban na APC ya rika yin katsalandan, don haka ya gargade shi da cewa ya guji tsoma masu baki a siyasar jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da PDP da ‘Jam’iyyar kayan marmari’ inji ‘Danuwan Buhari, Hon. Fatihu

Me ya yi zafi?

A cewarsa, Ahmad Lawan da aka mikawa INEC sunansa, sam bai cikin ‘yan takaran APC a zaben. Machina ya ce kage ne a ce shugaban majalisa ya shiga zabe.

Tsohon ‘dan majalisar ya ce su na da sakamakon zabe, kuma duk wani ‘dan Najeriya ya ga sakamakon zaben da aka fitar cewa Lawan bai yi takara ba.

"Duk wani mai hankali ya san ranar da aka kebe na wannan zaben tsaida gwani. Kuma kowa ya san an je aiwatar da wannan zabe." - Bashir Machina.

Bugu da kari, Hon. Machina ya ce ya kamata Sanata Adamu ya tsaya a matsayinsa na shugaban APC na kasa, ba shugaban wata kabila ko wanni bangare ba.

A karshe, Bashir Machina ya bukaci tsohon gwamnan na jihar Nasarawa da ya guji jagwalgwala jam’iyyar APC ta jihar Yobe, sannan ya nemi afuwarsa a fili.

An gaji da Lawan - Machina

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Kwanaki aka ji labari Bashir Machina ya ce duk da mutanen Lawan su na tuntubarsa, ba zai hakura da tikitinsa, shi ne 'dan takarar Sanata a Yobe ta Arewa.

'Dan siyasar ya koka a kan Ahmad Lawan, yake cewa mutanen yankin Arewacin Yobe sun gaji da shi, don haka zaben 2023 ya kamata wani ya wakilci mazabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel