Wata Jam'iyyar Najeriya Ta Sake Kaddamar Da Shahararriyar Jarumar Fina-Finai A Matsayin Mataimakiyar Gwamna

Wata Jam'iyyar Najeriya Ta Sake Kaddamar Da Shahararriyar Jarumar Fina-Finai A Matsayin Mataimakiyar Gwamna

  • Jam'iyyar African Action Congress (AAC) ta kaddamar da jarumar Nollywood, Coroline Hutchings aka Caroline Danjuma matsayin mataimakiyar gwamna a Akwa Ibom
  • Caroline Danjuma ta shiga jerin sauran jaruman fina-finai irinsu Tonto Dikeh da Funke Akindele wadanda suma aka zabe su yan takarar mataimakan gwamna a wasu jam'iyyu a zaben 2023
  • A sanarwar da ta fitar, AAC ta ce an zabi Caroline ne saboda kaunar mutane da ta ke yi, rayuwa ta gari da jajircewarta wurin inganta garuruwa a Akwa Ibom da iya jagoranci

An kaddamar da Jaruma Coroline Hutchings wanda aka fi sani da Caroline Danjuma a matsayin abokiyar takarar Mr Iboro Otu, dan takarar gwamna na jam'iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2023 a Akwa Ibom, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kutsa Gonar Tsohon Gwamna a Najeriya, Sun Sace Mai Kula Da Gonar

Caroline Danjuma
Wata Jam'iyya Ta Sake Kaddamar Da Shahararriyar Jarumar Fina-Fina A Matsayin Mataimakiyar Gwamna. Hoto: @carolynahutchings
Asali: Instagram

Jarumar ta shiga jerin sauran jaruman fina-finan kudu kamar Funke Akindele (PDP) da Tonto Diike (ADC) da suka zama mataimakan gwamna a zaben na 2023 da ke tafe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumar ta zama mataimakiyar shugaban kasar ne a jam'iyyar da dan jarida kuma mai rajin kwato hakkin bil-adama, Omoyele Sowore ya kafa.

Dalilin da yasa AAC ta zabi Caroline

A sanarwar da jam'iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na jiha da sakatare, Utip Etiebet da Gabriel Ekpo, AAC ta yi bayanin cewa an zabi Caroline ne saboda kaunar mutane da ta ke yi, rayuwa da ta dace da jajircewarta wurin inganta garuruwa a Akwa Ibom da iya jagoranci.

Wani sashi na sanarwar:

"A madadin jam'iyyarmu, ta African Action Congress da kungiyar yakin neman zaben gwamna na Iboro Otu, muna son sanar da yan jam'iyyar mu da mutanen Akwa Ibom da yan Najeriya yar takarar mataimakiyar gwamnan mu a zaben 2023 a zaben Jihar Akwa Ibom, Cif Mrs Caroline Uduak Danjuma.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

"Cif Mrs Caroline, Obong Uwana na Eket, yar kasuwa ce na kasa da kasa, jarumai wacce ta lashe lambobin yabo kuma mai taimakon alumma. Ta fito ne daga gidan basarake, Mai martaba, Edidem William Esiet Ekwere."

A bangarenta, jarumar ta Nollywood ita ma ta bada sanarwar a shafinta na Instagram, ta nuna hotonta da tambarin jam'iyyar AAC, ta kuma yi rubutu na yin addu'an Allah ya bata ikon yi wa Akwa Ibom da Najeriya hidima.

Ba Zan Daga Wa Gwamnatin Buhari Da Sauran Na Baya Kafa Ba, Sai Na Bincike Su, In Ji Sowore

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya ce gwamnatinsa za ta binciki gwamnatocin baya idan aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2023.

Sowore ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter @yeleSowore, a ranar Asabar.

Hakan ya ci karo da abin da Peter Obi dan takarar jam'iyyar LP ya furta na cewa ba zai binciki gwamnatocin baya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel