Ba Zan Daga Wa Gwamnatin Buhari Da Sauran Na Baya Kafa Ba, Sai Na Bincike Su, In Ji Sowore

Ba Zan Daga Wa Gwamnatin Buhari Da Sauran Na Baya Kafa Ba, Sai Na Bincike Su, In Ji Sowore

  • Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress a 2023 ya ce zai binciki gwamnatocin baya idan ya zama shugaban kasa
  • Mr Sowore ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar 9 ga watan Yuli
  • Dan gwagwarmayar ya ce idan har ana iya kwato kudade da marigayi Sani Abacha ya boye, dole a kwato na hannun shugabanni da ke raye

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya ce gwamnatinsa za ta binciki gwamnatocin baya idan aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2023.

Sowore ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter @yeleSowore, a ranar Asabar.

Sowore
Zan Bincike Gwamnatin Buhari Da Saura Idan Na Zama Shugaban Kasa, Sowore. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Peter Obi: Ba Zan Binciki Gwamnatin Buhari Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa

Hakan ya ci karo da abin da Peter Obi dan takarar jam'iyyar LP ya furta na cewa ba zai binciki gwamnatocin baya ba.

Ya ce:

"A matsayi na na shugaban Najeriya, Zan binciki gwamnatocin baya in karbo dukkan kudaden da tsaffin shugabanni suka sace, wadanda suka hallaka mutanen da ba su yi komai ba suka hana su rayuwa mai kyau. Idan za mu iya kwato daga Sanni Abacha da ya rasu, ya kamata a kwato daga barayi da ke raye."

Da ya ke sake wallafa sakon na Sowore, abokin takararsa, Haruna Magashi, ya kara da cewa:

"Babu wanda za a daga wa kafa, dukkan barayin yan siyasa, na baya da na yanzu za a tona musu asiri a gwamnatinmu. Dole a kwato kudaden da suka sace daga yan Najeriya."

Peter Obi: Ba Zan Binciki Gwamnatin Buhari Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa

A bangarensa, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ya ce ba zai binciki gwamnatin da ta shude ba idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa a 2023, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

Da ya ke magana a ranar Juma'a bayan gabatar da mataimakinsa Datti Baba-Ahmed, wanda ya kafa Jami'ar Baze. Obi ya ce zai mayar da hankali ne wurin dakile wuraren da ake asarar kudi da kuma ciyar da kasa gaba.

Obi ya ce ba zai yi wu ya rufe shago ya bi barawo da ya yi sata ba don haka zai mayar da hankali ne don gina kasa da toshe hanyoyin da ake satan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel