2023: APC, PDP Na Fuskantar Barazana A Yayin Da Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Farfesa Ango Abdullahi

2023: APC, PDP Na Fuskantar Barazana A Yayin Da Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Farfesa Ango Abdullahi

  • Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya taho kamfen a yankin arewacin Najeriya
  • Obi ya ziyarci shugaban kungiyar dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi sannan ya ziyarci garinsu mataimakinsa Datti Baba Ahmed
  • Dan takarar shugaban kasar na LP ya ce arewa yanki ne mai muhimmanci sosai a siyasar Najeriya don haka dole a tuntubi masu ruwa da tsaki a yankin

Jihar Kaduna - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya fara zuwa kamfen yankin arewacin Najeriya.

Obi, wanda ke da magoya baya sosai a dandalin sada zumunta ya ziyarci shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, Daily Trust ta rahoto.

Obi da Abdullahi.
2023: APC, PDP Na Fuskantar Barazana A Yayin Da Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Farfesa Ango Abdullahi. Peter Obi, Kanyi Daily.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha

Obi ya ziyarci garinsu mataimakinsa

Ya kuma ziyarci garinsu abokin takararsa, Dakta Datti Baba Ahmed.

Da ya ke magana da manema labarai jim kadan bayan ziyarar, Obi ya ce, "Na zo neman albarka ne da shawara daga iyaye da kuma tattauna wasu batutuwan siyasa da dattijon na kasa.
"Wannan ya dace da matsayinsa musamman a arewa da jajircewarsa na ganin an samu jagorancin demokradiyya mai kyau a kasar."
Obi ya ce daga cikin abubuwan da suka tattauna shine ganin yadda za a sauya kasar zuwa kasa mai rike kanta, domin ta dade a matsayin kasa na cimma zaune.
"Domin yanzu kasar bata samar da komai, Yan najeriya na cikin yunwa, babu ayyuka kuma mutane na neman sabon rayuwa. Duk da kasar noma a arewa, yan Najeriya na fama da yunwa saboda muna cigaba da dogara kan man fetur, muna watsi da albarkar kasa da muke da shi.
"Dole mu hadu mu gina sabuwar Najeriya, kasar da za ta yi wa dukkan mu aiki," in ji shi.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

Arewa na da muhimmanci a siyasar Najeriya, dole a tuntubi masu ruwa da tsakinta, Obi

A cewarsa, ana yi wa arewa kallon yanki mai muhimmanci a siyasa don tana da yawan mutane kuma za ta iya karkatar da akallar siyasar kasar don haka dole a tuntubi masu ruwa da tsaki a yankin don gina kasa mai kyau.

Ya shawarci yan Najeriya su yi tunani da basira kafin zaben shugabanninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel