2023: Jam’iyyar APC ta ba Mutumin da yake da Digiri 6 takarar Mataimakin Gwamna

2023: Jam’iyyar APC ta ba Mutumin da yake da Digiri 6 takarar Mataimakin Gwamna

  • APC ta tsaida Idris Muhammad Gobir a matsayin ‘Dan takaran mataimakin gwamnan Sokoto
  • An bada sanarwa cewa Idris Muhammad Gobir shi ne Abokin takarar Ahmed Aliyu a zaben 2023
  • Gobir ya yi aiki da Ministan tarayya, sannan ya taba rike Kwamishina da Kantoma a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Sokoto, ta kaddamar da Idris Muhammad Gobir a matsayin ‘dan takarar mataimakin gwamna a zabe mai zuwa.

Punch ta kawo rahoto a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli 2022 da ya tabbatar da cewa Alhaji Idris Muhammad Gobir ne abokin takarar Ahmed Aliyu.

Shugaban APC na jihar Sokoto, Alhaji Isa Acida ya shaidawa manema labarai cewa ‘Dan takarar gwamna na 2023 ya yanke hukunci ya dauki Isa Gobir.

Idris Muhammad Gobir ya taba rike mukamin Mai ba Ministan harkokin ‘yan sanda na kasa watau Muhammad Dingyadi Maigari, shawaran musamman.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya fito yana adawa da takarar Musulmi-Musulmi

Gobir tsohon Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ne a jihar Sokoto. Rahoton ya ce ya taba rike Kantoma na karamar hukumar Sabon Birni.

Sun ta ce Gobir ya yi aiki a baya a gwamnatin tarayya a hukumomin DPR da NPA.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam’iyyar APC
APC ta na kamfe a Sokoto a 2019 Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC

Idris Muhammad Gobir ya na da Digiri 6

‘Dan siyasar mai shekara 47 ya yi Digirinsa na farko ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Baya ga Digirin farko da ya yi a ABU, ‘dan takaran mataimakin gwamnan yana da shaidar digirgir a fannoni har biyar da suka hada da ilmin cigaban al’umma.

Haka zalika Isa Gobir wanda zai rike tutar APC a Sokoto ya na da shaidar digiri na biyu a bangarorin kula da manhajar komfuta da ilmin huldar kasashe.

Da yake gabatar da jawabin amincewa da takara, Gobir ya yi godiya na musamman ga ‘dan takarar gwamna watau Ahmed Aliyu da jigon APC, Aliyu Wammako.

Kara karanta wannan

Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC

Gobir ya yi godiya da sauran masu ruwa da tsaki a APC ta jihar Sokoto, ya kuma yi alkawarin cewa ba zai ci amanar wadanda suka ba shi wannan takara ba.

Tambuwal zai nemi Sanata

Kwanakin baya kun samu rahoto cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai shiga takarar Sanata a majalisar Dattawa bayan ya rasa tikitin shugaban kasa.

A zaben gwamna, za a gwabza ne musamman tsakanin APC da PDP. Gobir Umar Sa’adu, da Sagir Bafarawa za su yi wa PDP mai mulkin jihar takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel