Gwamna Tambuwal zai koma wata takarar ganin zama Shugaban kasa a PDP ya gagara

Gwamna Tambuwal zai koma wata takarar ganin zama Shugaban kasa a PDP ya gagara

  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai shiga takarar Sanata a majalisar Dattawa a zaben 2023
  • Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal yana cikin wadanda suka nemi tikitin shugaban kasa a PDP
  • Babu mamaki jam’iyyar PDP ta canza ‘dan takarar Sanatanta a shiyyar kudancin jihar Sokoto

Sokoto - Alamu na nuna cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai nemi takarar Sanata na mazabar kudancin jihar Sokoto a zabe mai zuwa na 2023.

Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto bayan kusan mako daya kenan da Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya janye neman takarar shugaban kasa.

A tsakiyar shekara mai zuwa wa’adin Gwamnan na Sokoto zai cika, zai sauka daga karagar mulki.

Wannan ta sa Aminu Waziri Tambuwal ya fara hangen yin takarar Sanata a karkashin jam’iyyar PDP, zai karbe tikiti ne daga hannun Aminu Bala Bodinga.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya shiga tsakanin shugabannin PDP bayan Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban kasa

Tsohon kwamishinan na gidaje da safayo na jihar Sokoto, Aminu Bala Bodinga shi ne wanda ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na PDP na Sanatan.

Aminu Bondinga zai yi waje?

Tun a baya an yi tunanin Aminu Bodinga ya rike tikitin ne kafin ganin yadda sakamakon zaben fitar da gwanin shugaban kasa zai kasance a jam’iyyar PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Tambuwal
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a taron PDP Hoto: @Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Ganin Tambuwal bai yi nasara ba, Bodinga zai iya ba Mai gidansa wuri ko kuma jam’iyyar ta gudanar da wani sabon zaben fitar da gwani na Sanata.

Rahoton ya nuna Bodinga yana cikin manyan na-kusa da Tambuwal a siyasa. Tun 2015 ya ke tare da Gwamnan a lokacin yana ‘dan majalisa na Bodinga.

Bayan Rt. Hon. Tambuwal ya fice daga APC zuwa PDP a 2018, Bodinga yana cikin wadanda suka biyo shi. A 2019 ya nada shi kwamishina bayan fadi zabe.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu

Da farko Bodiga ya rike kwamishinan matasa da wasanni, daga baya aka canza masa ma’aikata.

A halin yanzu Sanata Ibrahim Danbaba ne yake rike da wannan kujera. Shi kuwa tuni ya koma APC, bayan an samu sabani tsakaninsa da Gwamnan a PDP.

'Yan siyasa su na raba kafa

Tun a watan da ya wuce ku ka ji labari akwai ‘yan siyasan da ake tunanin za su shiga takara biyu da dabara saboda gudun bacin-rana wajen zaben tsaida gwani.

A lokacin kun ji ana zargin Aminu Bodinga ya saye fam ne da sunan Aminu Tambuwal. Idan Gwamnan bai samu tikitin shugaban kasa ba, zai nemi Sanata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel