Atiku: Sai da APC da su Buhari suka dawo da Najeriya baya cikin shekaru 7 kacal

Atiku: Sai da APC da su Buhari suka dawo da Najeriya baya cikin shekaru 7 kacal

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP ya caccaki yadda APC ta mai da Najeriya baya a karkashin mulkinta na farko da na biyu
  • Atiku ya kuma bayyana cewa, a Najeriya akwai siyasar bangaranci mara dalili, kuma dole a kawo karshenta
  • A bangare guda, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai dashi domin ganin karshen mulkin su Buhari a 2023

Najeriya - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, a ranar Lahadi ya magantu, ya bayyana cewa Najeriya a karkashin APC, ta ga mafi munin yanayi na siyasa kuma na bangaranci.

Atiku, a cikin wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, ya yi nuni da cewa akwai bukatar a kaucewa ra'ayi da bangaranci a wani yunkuri na karfafa hadin kan kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ga Tinubu: Ka bi a hankali, ka kula da lafiyarka, ka bar mu da kamfen

Atiku ya caccaki APC, ya ce ta tsoma Najeriya a matsalar gaske
Atiku: Sai da APC da su Buhari suka durkusar da Najeriya cikin shekaru 7 kacal | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai tare dashi wajen tabbatar da hadin kan dukkan bangarorin kasar nan tare da tafiya tare, a kuma tsira tare

A kalaman Atiku kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A irin wannan lokaci da kasarmu ke cikin mawuyacin hali, yana da kyau mu daina barin kowane irin ra’ayin bangranci ya mamaye siyasarmu.
"Ana son siyasa ta zama hanyar gyara ne. Don haka, ko da muna jin haushin kaskanci mara dalili da jam’iyyar APC mai mulki ta jefa mu cikin shekaru bakwai da suka gabata, dole ne mu tabbatar mun killace siyasarmu daga gurbatar gazawar jam’iyya mai mulki. Al'umma ba za ta ci gaba ba idan siyasarta ta dagule.
“Ya kai abokina kuma dan kasa, tafiyar da muka hada hannu domin gudanar da ita tare, ba tafiya ce wadda za mu cimma ta hanyar gwama ta da siyasar bangaranci ba. Wannan tafiya, yakin neman zabenmu, manufa ce ta ceto ga babbar kasarmu kuma manufa ce da ta shafi dukkan 'yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

Da yake bayyana irin tsarin siyasarsa, Atiku ya ce, yayin da APC ke kokarin sake komawa mulki a 2023 ta wacce hanya, shi nasa salon zai zama shugaba ne ta hanyar hada kan 'yan Najeriya.

Bikin sauya sheka: Dan majalisa ya fice daga APC, ya shige inuwar leman PDP

A wani labarin, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ogo-Oluwa/Surulere a majalisar dokokin jihar Oyo, Honarabul Simeon Oyeleke ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, inji rahoton Tribune Online.

Oyeleke, wanda aka zaba a majalisar wakilai ta yanzu a karkashin jam’iyyar APC ya bayyana matakin nasa ne a ranar Laraba 6 ga watan Yuli, 2022.

Oyeleke dai ya bayyana dalilin ficewarsa ne ga gazawar jam’iyyar APC a jihar Oyo wajen tabbatar da adalci da daidaito wajen mu’amala da 'yan jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel