Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023

Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki a kasa a zaben 2023, Bola Tinubu ya bayyana dalilin da yasa bai zabi abokin takara kirista ba
  • Tinubu ya ce duk tsawon rayuwarsa cancanta, gaskiya, adalci, tausayi da iya aiki ya ke duba wa wurin zaben masu aiki tare da shi ba addini ba ko yanki
  • Tsohon gwamnan na Jihar Legas ta nuna cewa ya saurari koken da bangarori daban-daban suka yi kan batun amma daga karshe ya dauki mataki mai wahala wanda ya ke ganin shine ya fi dacewa ga cigaban kasa

Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2023 ya kare zabinsa na Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takara, Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shettima bai san shine abokin takarata ba, in ji Tinubu

Kafin bayyana Shettima a matsayin mataimaki, siyasar kasar ta dauki zafi kan batun zaben yan takara masu addini iri daya.

Tinubu da Kashim.
Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023. Hoto: @channelstv.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta yi gargadin hakan, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya su mayar da hankali kan cancanta fiye da addini ko kabila.

Dalilin zaben Shettima

Da ya ke magana kan dalilin zaben Shettima a matsayin abokin takararsa, Tinubu ya ce a duk rayuwarsa, cancanta, basira, tausayi, gaskiya, adalci da kwarewa ne ya ke amfani da su wurin zaben tawagarsa da masu taimaka masa.

Ya ce ya tuntubi mutane da dama game da batun mataimakin kuma ya godewa manyan mambobin jam'iyyar da abokansa na siyasa da manyan kasa "wadanda ke yi wa Najeriya kallo irin nasa."

Tinubu ya fayyace cewa bawa cancanta fifiko wurin shugabanci, da iya aiki tare da mutane shine babban abin da yasa ya zabi abokin takarar nasa.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

"Ina sane ta tattaunawa da ake yi game da addinin abokin takara ta. Mutanen kirki sun mana magana kan hakan. Wasu sun shawarci in dauki kirista saboda kiristoci, wasu sun ce in zabi musulmi saboda al'ummar musulmi. Tabbas ba zai yiwu in yi duka biyun ba."
"Bangarorin biyu suna da dalilansu. Dukkkansu suna da gaskiya a ra'ayinsu. Amma dukkansu ba abin da Najeriya ke bukata ba kenan a yanzu. A matsayin shugaban kasa, ina fatan mulkan Najeriya don samun cigaba. Hakan na bukatar sabbin dabaru. Hakan zai bukaci abin da ba a yi ba a baya. Zai bukaci matakan siyasa masu wuyan zartarwa da ba a saba gani ba.
"Idan zan zama irin wannan shugaban kasar, dole in fara da zabin mataimaki na. Bari in dauki mataki ba don siyasa ba amma don bunkasa kasa da jam'iyyar mu don cigaba.
"A nan siyasa ta zo karshe, kuma ainihin jagorancin ya fara. Yau, na sanar da mataimaki na kuma ba don addini na zabe shi ba ko dan faranta wa wani bangare rai. Na zabe shi ne don na yi imanin zai taimaka min wurin gudanar da ingantaccen mulki, ba tare da la'akari da addini, kabila ko yanki ba."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara, CAN ta yi martani

Ga wanda ba su ji dadin zabin Tinubu ba, ya ce ba wai baya sauraren kokensu bane yana sane da su domin hakan na cikin mulki na gari amma ba kowanne lokaci bane addini da kabilanci zai rika jagorancin abin da za mu yi.

Domin cigaba dole mu yi watsi da wasu abubuwan baya mu daidaita siyasarmu kan turban cancanta da adalci ba wai yanki ba.

Liman Ya Yi Wa Kwankwaso Kamfen A Wurin Sallar Idi, Ya Ce Shine Dan Takara Mafi Cancanta a 2023

A wani rahoton, Sheikh Muhammadu Aminudeen, babban limamin masallacin Juma'a na Daawah, Kano, ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kara kaimi a yakin neman zabensa na shugabancin kasa.

Babban limamin, wanda da ne ga marigayi Sheikh Aminudeen Abubakar, shaharraren malamin addinin musulunci a Kano kuma wanda ya kafa Kungiyar Daawah ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel