Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

  • Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya goyi bayan dan takarar APC, Bola Tinubu, na yin tikitin Musulmi da Musulmi a kokarinsa na son gaje Buhari
  • Ladoja ya ce babu aibu don mabiya addinai guda sun daga tutar jam’iyya daya a zaben shugaban kasa
  • Sai dai kuma, yana jimma Tinubu tsoron kada a maimaita abun da ya faru da MKO Abiola a 1993

Oyo - Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya bayyana cewa babu wani aibu wajen tsayar da Musulmi da Musulmi domin zama shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023.

Da yake magana a gidansa da ke Bodija, Ibadan jim kadan bayan sallar Idi, tsohon gwamnan ya ce bai kamata ra’ayin Musulmi da Musulmi ya zama cikas wajen zabar shugabanni ba, jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara, CAN ta yi martani

Ya ce zabar dan takara da ya cancanta bai da alaka da makomar addinin mai shi.

Tinubu da Ladoja
Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga wani tsohon gwamna Hoto: Guardian
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci yan Najeriya da su yi watsi da banbancin addini sannan su mayar da hankali wajen zabar dan takarar da ya cancanta da kuma tarihi mai kyau, jaridar The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ladoja ya kuma bayyana cewa tsoron yan Najeriya yana kewaye ne da yanayin rashin tsaro da kasar ke fama da shi a yanzu karkashin jagorancin Musulmi wato shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ladoja na jima Tinubu tsoron maimaicin abun da ya faru da Abiola

Ya kuma bukaci yan Najeriya da su ci gaba da yiwa Bola Tinubu addu’a a kokarinsa na son zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Ladoja ya bayyana cewa yiwa Tinubu addu’a na da muhimmanci sosai don kada abun da ya faru da marigayi Bashorun Moshood Abiola a zaben 1993 ya sake maimaita kansa.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahemd ya bayyana dalilin da yasa ya amince ya zama abokin takarar Obi

Ya ce:

“Akwai abubuwa da yawa a zaben shugaban kasa. Duk wanda ke son zama shugaban kasa da masu yi masa aiki dole ne su yi aiki tukuru. A zahiri, za su bukaci karin addu'a yayin da suke tuntuba. Da wannan kokari, Allah ne ke da ikon zabar wanda zai zama shugaban kasa. Cif MKO Abiola, wanda Musulmi ne an zabe shi tare da mataimakinsa, Musulmi.
“Kawai muna addu’a cewa idan Tinubu ya yi nasara, kada abun ya zama irin na Marigayi MKO Abiola. Ban ga wani aibu a tikitin Musulmi da Musulmi ba, saboda bana sanya baki a lamuran addini.”

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa addinin Islama ko Kiristanci bai da hurumi a siyasa. Ya ce dukkanin addinan biyu Allah daya suke bautawa.

2023: Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara, CAN ta yi martani

Mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya amince da daukar Musulmi a matsayin abokin takararsa gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

2023: PDP ta yi dabara, ta zabo wanda zai kawo karshen APC a Gombe, inji tsagin dan takara

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli, a yayin bikin babban Sallah a jihar, Daily Independent ta rahoto.

Tinubu ya dauki Alhaji Kabir Ibrahim Masari, dan siyasar Katsina, a matsayin mataimaki na wucin gadi domin cike wa’adin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta diba masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel