PDP ta cika da fargaba sakamakon ganawar da ya gudana tsakanin Wike da gwamnonin APC

PDP ta cika da fargaba sakamakon ganawar da ya gudana tsakanin Wike da gwamnonin APC

  • Wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party, na nuna halin ko in kula da abubuwan da Gwamna Wike ke yi
  • A bangare daya kuma wasu yan PDP sun damu cewa yana iya sauya sheka sakamakon ganawarsa da APC
  • Jigon PDP, Maina Waziri, ya zargi tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da kitsawa Wike maganganu

Ganawar gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, da wasu gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ake ganin makusantan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu ne ya haifar da fargaba a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Manyan jiga-jigan APC da suka gana da Wike sun hada da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo Olu, da kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Gwamna Fayemi, Babajide Sanwolu da Rotimi Akeredolu sun kai wa Wike ziyara a Fatakwal

Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Ekiti wanda ya kasance dan PDP, Ayodele Fayose ma ya halarci taron wanda ya gudana a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Wike da gwamnonin APC
PDP ta cika da fargaba sakamakon ganawar da ya gudana tsakanin Wike da gwamnonin APC Hoto: Leadership News
Asali: Facebook

Tuni wasu manya-manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP suka fara tofa albarkacin bakunan a kan lamarin, inda wasu ke fargabar ko Gwamna Wike zai sauya sheka ne daga jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kuma na ganin ficewarsa daga jam’iyyar adaware zai shafi karfin da jam’iyyar ke da shi a babban zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani dan kwamitin uwar jam’iyya ta PDP wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce jam’iyyar ta fi karfin kowani mutum.

Ya ce:

“PDP ta nan tun 1998. Mun ga mambobi iri-iri da suka zo kuma suka tafi.
“Tare da mutunta kowa, kasancewa dan jam’iyyar nan ra’ayi ne. Za mu so samun mutane a kasa, amma za mu fi inganta da wadanda suka yarda da manufar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kungiyar TAM ta nesantar da Atiku daga rikicin bangarancin PDP a jihar Ekiti

“Bana tunanin akwai wata sadaukarwa da za a ce ta yi yawa daga mambobin jam’iyya don ganin mun koma mulki a 2023.
“Eh, shakka babu, jihar Rivers na daya daga cikin wuraren da muke da karfi kuma mun ba jihar da mutanenta mutuntawar da suka cancanci samu.
“Amma babu mutumin da zai iya garkuwa da jam’iyyar. Siyasa ra’ayi ne kuma ra’ayinmu a matsayin jam’iyya a yanzu shine yadda za mu lashe zabe mai zuwa don ceto kasar nan da dukkanmu muke so daga kangin da APC ta shigar da mu.”

Haka kuma, wani dan PDP ya ce batun sauya shekar Gwamna Wike na tsorata shi.

Jigon na PDP wanda ya nemi a boye sunansa da aka tambaye shi ko ya damu sai ya ce:

“Shakka babu, waye ba zai damu ba? Zaben 2023 saura yan watanni kadan ne. muna bukatar dukkanin jajirtattun mambobinmu.”

Waziri ya zargi tsohon gwamna Fayode da zuga Wike

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Osun: Buhari ya karbi bakuncin Oyetola, ya ce APC ce za ta lashe zaben

Wani mamba na kwamitin amintattu na PDP, Maina Waziri, a wata hira da aka watsa a Arise Television a ranar Juma’a, ya zargi tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da zuga Wike.

Waziri ya ce:

“Mutum na farko da ya kawowa PDP cikas a Ekitis shine Fayose, wanda ke yiwa APC aiki. Mun rigada mun san yana tare da Bola Tinubu don yiwa APC aiki."

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya bayyana cewa babu wani aibu wajen tsayar da Musulmi da Musulmi domin zama shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023.

Da yake magana a gidansa da ke Bodija, Ibadan jim kadan bayan sallar Idi, tsohon gwamnan ya ce bai kamata ra’ayin Musulmi da Musulmi ya zama cikas wajen zabar shugabanni ba, jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban APC na shiyyar wata jiha da dubba mambobin sun koma PDP

Ya ce zabar dan takara da ya cancanta bai da alaka da makomar addinin mai shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng