Yarbawan Arewa sun ba Tinubu shawarar daukar Fasto, Masoya sun ce a je da El-Rufai

Yarbawan Arewa sun ba Tinubu shawarar daukar Fasto, Masoya sun ce a je da El-Rufai

  • Kungiyar Coalition of Northern Yoruba Youths ta na so Bola Tinubu ya dauki Rabaren Yakubu Pam
  • CNYY ta ce Yakubu Pam ya dace ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • ‘Yan tafiyar APC Media and Mobilisation for BAT’23 sun bada shawara a dauki Gwamnan Kaduna ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wata kungiya mai suna Coalition of Northern Yoruba Youths (CNYY) ta ba Bola Tinubu shawarar ya zabi Yakubu Pam a matsayin mataimakinsa.

Wannan kungiya mai suna CNYY ta na ganin Rabaren Yakubu Pam zai dace da ‘dan takaran APC a zaben 2023, Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoton.

CNYY ta bayyana wannan zabi da ta dauka ne a karshen wani taro da ta shirya a garin Kaduna.

Kungiyar ta ke cewa lura da tafiyar Bola Tinubu a siyasa, zai yi kyau ya dauko Yakubu Pam a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

Direbobin Keke-Napep sun fadawa Bola Tinubu wanda ya kamata ya tafi da shi a APC

Yakubu Pam ya cancanta inji CNYY

An rahoto shugabannin kungiyar matasan Arewa watau Coalition of Northern Yoruba Youths ta na cewa Yakubu Pam zai sa Tinubu ya kai labari a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban CNYY na kasa, Deji Abdullateef da Sakatarensa, Ajayi Johnson suka sa hannu a takardar da aka fitar bayan zaman da matasan suka yi a jiya.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da 'Yan APC da zaben Ekiti Hoto: officialasiwajubat
Asali: Facebook

Wasu Matan Jam'iyya sun bi Pam

Leadership ce wata kungiyar matan APC na da ra’ayin cewa muddin Tinubu ya hada tikitin neman shugaban kasa da Rabaren Pam, hakan zai taimaka masa sosai.

Shugaban kungiyar matan, Lady Princess Ajibola ta yabi shugaban hukumar Nigerian Christian Pilgrimage Commission, ta ce ya dace a ba shi takara.

Wannan zabin ba da mu ba

A gefe guda, an samu rahoto wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ba su tare da kungiyar matasan a kan wannan zabi da suka yi na daukar wannan Fasto.

Kara karanta wannan

Za a jikawa Jam’iyyar APC aiki, an maka IGP a kotu kan binciken Tinubu da aka yi a 1999

Daily Trust ta ce kungiyar nan ta APC Media and Mobilisation for BAT’23 masu yada takarar Bola Tinubu a APC sun bada shawarar a dauki Nasir El-Rufai.

Kungiyar APC Media and Mobilisation for BAT’23 ta reshen jihar Kaduna ta ce babu wanda ya dace ya zama mataimakin Tinubu kamar Gwamna El-Rufai.

Wannan kungiya ta roki shugabannin APC su bada shawarar a ba El-Rufai tikitin mataimaki. A yanzu saura mako daya wa’adin tsaida ‘dan takara ya cika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel