Yanzu-Yanzu: Shugaban APC na shiyyar wata jiha da dubban mambobi sun koma PDP

Yanzu-Yanzu: Shugaban APC na shiyyar wata jiha da dubban mambobi sun koma PDP

  • Shugaban jam'iyyar APC a shiyyar Ibadan ya bayyana ficewa daga jam'iyyar, ya kuma ja zuga da yawa
  • Hakazalika, wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar ta APC sun sauya sheka, kuma sun bayyana shiga jam'iyyar PDP
  • Komawarsu PDP na da nasaba da nuna goyon baya ga gwamnan Oyo mai ci, Seyi Makinde, kamar yadda rahoto ya ce

Ondo - Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Bashiru Ajibade, ya jagoranci daruruwan ‘ya’yan jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, Leadership ta ruwaito.

Taron wanda ya gudana a makarantar IMG, Eleta, ya kuma nuna ficewar manyan masu ruwa da tsaki na APC kamar su Alhaji Abass Najeemdeen Gbayawu, Alhaji Bolaji Akinyemi Kosigiri, Engr Kayode Arowolo, da Barista Rotimi Okeowo da dai sauransu.

Shugaban APC ya tattari zuga, sun koma jam'iyyar PDP
Yanzu-Yanzu: Shugaban APC na shiyyar wata jiha da dubban mambobin sun koma PDP
Asali: UGC

Da yake magana a madadin shugabannin da suka sauya shekar, Prince Olumuyiwa Akinbiyi ya bayyana cewa ba su gamsu da yadda APC ta gudanar da zabukan fidda gwani na APC da wasu ‘

Kara karanta wannan

Babu ruwanmu da kai namu ne: Jiga-jigan APC a mahaifar Atiku sun sha alwashin ganin bayansa a zaben 2023

A cewarsa, suna barin jam’iyyar APC ne tare da mafi yawan mambobinta a kananan hukumomin domin marawa takarar gwamna Seyi Makinde baya ya sake tsayawa takara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wadanda suka sauya shekar sun samu tarba ne a madadin Gwamna Makinde ta hannun Cif Bayo Lawal, da babban darakta na yakin neman Seyi Makinde.

Hakazalika da shugaban karamar hukumar Ibadan ta kudu maso gabas, Emmanuel Alawode da Kazeem Adeniyi Bibire, S.A. ga gwamna kan harkokin kananan hukumomi da sarautun gargajiya.

Zaben 2023: APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo da za ta sa a dama da matasa a siyasa

Jam’iyyar APC mai mulki ba shirya wasa ba, domin ta shirya kaddamar da shafin yanar gizo domin hada kan matasa kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana shirin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni a Abuja.

Kara karanta wannan

Saba alkawari: Ta karewa APC a Sokoto, 'yan kasuwa sun yi watsi da ita sun koma PDP

Mista Israel ya bayyana cewa sabon shirin an yi shi ne domin tabbatar da damawa da matasa a harkokin siyasar jam'iyyar. Ya ce dandali ne da ake son amfani dashi wajen jawo hankalin matasa zuwa jam’iyyar.

Ya ce:

“Za mu hada hannu da dukkan manyan mashawarta na musamman (SSA) da masu ba da shawara na musamman kan matasa a fadin jihohi 36 na kasar nan, ciki har da babban birnin tarayya (FCT)."

Gabanin 2023: ‘Yan kasuwan Sokoto sun bar APC sun kama PDP bisa saba alkawuran APC

A wani labarin, 'yan kasuwa a Sokoto sun fice daga APC zuwa PDP saboda rashin cika alkawura da APC ta yi wa Kungiyar matasan ‘yan kasuwan jihar Sokoto.

Sun koma PDP, jam'iyya mai mulki a jihar domin marawa tafiyar jam'iyyar baya a zabuka da ke tafe a 2023.

Rahoton Daily Trust ya ce, ’yan kasuwar da suka yi tir da kasancewarsu a jam’iyyar APC sun yi ficewarsu daga cikinta ne a cibiyar tarihi da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

Asali: Legit.ng

Online view pixel