Babu ruwanmu da kai namu ne: Jiga-jigan APC a mahaifar Atiku sun sha alwashin ganin bayansa a zaben 2023

Babu ruwanmu da kai namu ne: Jiga-jigan APC a mahaifar Atiku sun sha alwashin ganin bayansa a zaben 2023

  • Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Adamawa sun sha alwashin hana ruwa gudu ta bangaren Atiku Abubakar a 2023
  • Shugabannin jam’iyyar mai mulki a kasar sun dauki alkawarin hana dan takarar shugaban kasa na PDP kai labari a babban zabe mai zuwa
  • Sun kuma nuna karfin gwiwar cewa yar takarar gwamnarsu, Sanata Aishatu Binani za ta lallasa gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri a zaben

Adamawa - Manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa sun jadadda jajircewarsu na zuwa gida-gida don yin kamfen a kokarinsu na son ganin jam’iyyarsu ta lashe dukkanin mukaman siyasa a jihar a 2023.

Masu ruwa da tsakin na APC karkashin inuwar ALGON wacce ta kunshi kananan hukumomin jihar 21 a yayin wata tattaunawa da shugaban jam’iyyar, Mallam Jamilu Yusuf, sun ce za su yi aiki ba ji ba gani don ganin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sha kaye a jihar.

Kara karanta wannan

Mance da su Ganduje da El-Rufai: Ka zabi abokin takara da Arewa ta tsakiya, jiga-jigan APC ga Tinubu

Atiku Abubakar
Babu ruwanmu da kai namu ne: Jiga-jigan APC a mahaifar Atiku sun sha alwashin ganin bayansa a zaben 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cewarsu, su yayan jam’iyya ne na gaskiya, kuma suna yiwa jam’iyyar biyayya a matsayinsu na masu tattara mutane daga tushe.

Sun kuma bayyana cewa goyon bayansu ga jam’iyyarsu zai sa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP shan kaye a Adamawa duk da kasancewarsa dan jihar, jaridar Thisday ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, sun jadadda cewa yar takarar gwamnan jam'iyyar a jihar, Sanata Aishatu Ahmed Dahiru Binani, za ta baiwa gwamna mai ci, Ahmadu Umaru Fintiri ciwon kai sosai.

Sun bayyana yadda PDP ta gaza samun sukuni saboda Binani sannan suka sauya mataimakin gwamnansu daga namiji zuwa mace. Sun kuma nuna karfin gwiwar cewa Binani za ta lallasa Fintiri a zaben.

Shugabannin kananan hukumomin 21 sun tattauna da wanda ya shirya taron, Jamilu, bayan ya gayyace su don neman hanyoyin da jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa a hade gabannin zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamna a Kaduna ya hada kai da 'yan Shi'a don nemawa Peter Obi kuri'u

Shugaban kungiyar ta ALGON, wanda ya kuma kasance shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Girei, Abubakar Audu, ya kuma bayyana cewa APC a Adamawa ta shirya ma aikin lallasa Atiku Abubakar a jiharsa, Daily Post ta rahoto.

Sai dai kuma, ya nuna damuwa cewa zaben fidda gwanin da aka yi ya fi amfanar deliget wadanda da wuya su kawowa jam’iyyar kuri’a daya fiye da su da suke matsayin sojojin yakin jam’iyyar.

2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal

A gefe guda, mun ji a baya cewa tohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa Bola Tinubu zai kayar da Atiku Abubakar a jihar Adamawa a babban zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da Atiku, wanda zai daga tutar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sune manyan yan takara a zaben kasar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Dubban mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a wata jahar arewa

Ana sanya ran Atiku wanda ya kasance dan asalin Adamawa ya kawo jihar a zabe mai zuwa amma tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce sam hakan ba mai yiwuwa bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel