Mance da su Ganduje da El-Rufai: Ka zabi abokin takara daga Arewa ta tsakiya, jiga-jigan APC ga Tinubu

Mance da su Ganduje da El-Rufai: Ka zabi abokin takara daga Arewa ta tsakiya, jiga-jigan APC ga Tinubu

  • Har yanzu jam’iyyar APC bata dauki wanda zai zama abokin takarar Asiwaju Bola Tinubu, dan takararta na shugaban kasa a 2023 ba
  • A yanzu haka, masu ruwa da tsaki daga yankin arewa suna ta kai ruwa rana a tsakaninsu kan wanda Tinubu zai zaba a matsayin abokin takararsa
  • Yayin da suke fafutukar samun gurbin mataimakin shugaban kasa, jam’iyyar na fama da sauye sauyen sheka a sauran yankunan kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Yayin da ake ci gaba da muhawara game da wanda zai zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wata kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa maso gabas ta bukaci jam’iyyar da ta dauki wanda zai dare wannan kujera daga arewa ta tsakiya.

A cewar masu ruwa da tsakin, wannan zai ba jam’iyyar damar lashe zaben shugaban kasa na 2023. Sun kuma bayyana cewa hakan zai nuna adalci, daidaito da gaskiyar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kungiyar Afenifere tayi kira ga jiga-jigan yan siyasan Yarabawa su marawa Tinubu baya

Tinubu
Mance da su Ganduje da El-Rufai: Ka zabi abokin takara da Arewa ta tsakiya, jiga-jigan APC ga Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Kungiyar ta masu ruwa da tsaki a Arewa maso gabas ta yanke wannan shawarar ne a Abuja a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli, yayin wani taron gaggawa da ya samu halartan mutane da dama.

Bukatar yankin arewa maso gabas

A wata sanarwa da aka aikewa Legit.ng, masu ruwa da tsaki daga Arewa maso yamma sun nuna sha’awarsu ga kujerar mataimakin shugaban kasa, inda suka bukaci APC da ta zabi nasu a matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron a Abuja a ranar Lahadi, Alhaji Abba Aji Suleiman, shugaban kungiyar ta arewa maso gabas na kasa, ya soki bukatar takwarorinsu na Arewa maso yamma, inda ya bayyana shi a matsayin rashin tunani.

Kungiyar ta yi korafin cewa:

Kara karanta wannan

Tinubu, zai bayyana Shettima ko Zullum a matsayin mataimakinsa

“Yankin Arewa maso yamma ta kasance rike da kambun mulki a shekaru bakwai na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma sake neman wannan kujerar ya nuna rashin tunani irin nasu.
“Ra’ayin masu ruwa da tsaki a yankin Arewa maso gabas shine cewa zai zama adalci ne kawai idan aka mika kujerar mataimakin shugaban kasa yankin arewa ta tsakiya, duba ga tarin gudunmawar da yankin ya bayar wajen ci gaban jam’iyyar.”

Ya kamata a baiwa Arewa ta tsakiya kujerar mataimakin shugaban kasa

Ya kara da cewa yankin Arewa ta tsakiya bata samu damar fitar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba duk da tarin nagartattun yan takarar da ke yankin.

Don haka ya bukaci APC da ta yi la'akari da mika kujerar mataimakin shugaban kasar ga yankin kamar yadda yankinsa ya yarda da hakan don yin adalci.

Da yake ci gaba da jawabi, Alhaji Suleiman ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

“Masu ruwa da tsaki na APC a Arewa maso gabas na fatan amfani da wannan kafar wajen kira ga shugabancin jam’iyyarmu don tabbatar da adalci da daidaito ta hanyar ba Arewa ta tsakiya mukamin mataimakin shugaban kasa.”

Saboda tsaro: Kungiya ta gargadi APC da Tinubu kan tikitin Musulmi da Musulmi

A wani labarin kuma, wata kungiya mai muradin kare damokradiyyar kasar ‘Nigeria Democracy Defence Watch’ ta roki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, da su yi watsi da shirin gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.

Punch ta rahoto cewa kungiyar ta yi wannan rokon ne a cikin wata wasika da ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari mai taken: “Tikitin Musulmi da Musulmi na APC a zaben Najeriya na 2023: Barazana ga kwanciyar hankalin kasa, zaman lafiya da tsaro.”

An gabatar da wasikar wacce ke dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Ahmed Adamu da Otunba Adeniji Adegoke, ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel