Mataimakin Gwamnan APC Da Ake Rade-Radin Zai Fita Daga Jam'iyyar Ya Yi Karin Haske

Mataimakin Gwamnan APC Da Ake Rade-Radin Zai Fita Daga Jam'iyyar Ya Yi Karin Haske

  • Mr Kelechi Igwe, mataimakin gwamnan Jihar Ebonyi ya karya jita-jitan cewa yana shirin ficewa daga APC ya koma Labour Party
  • Igwe, cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa Monday Uzor ya ce wasu yan adawa ne masu neman tada zaune tsaye suka yada jita-jitar
  • Igwe ya yi kira ga mutanen Jihar Ebonyi musamman magoya bayan APC su yi watsi da labarin su san cewa yana nan a jam'iyyarsa ta APC daram-dam

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ebonyi - Mataimakin gwamnan Jihar Ebonyi, Kelechi Igwe, ya ce ba ya shirin ficewa daga jam'iyyar APC zuwa Labour Party.

Hadiminsa, Monday Uzor, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abakaliki, Premium Times ta rahoto.

Mataimakin Gwamnan Ebonyi
Mataimakin Gwamna APC Da Ake Rade-Radin Zai Fita Daga Jam'iyyar Ya Yi Karin Haske
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: Sanata ya tona asirin wasu gwamnonin APC da suka dagula tsarin APC

Wani rahoto da aka wallafa a dandalin sada zumunta ya ce Mr Igwe ya kammala shirin fita daga APC.

Mr Uzor ya bayyana labarin a matsayin karya 'kuma yunkurin bata wa kujeran mataimakin gwamna suna da shi kansa.'

"Abin takaici ne wanda ya ke yada rahoton, kasancewarsa dan asalin Ebonyi ne, da gangan ya ke son ya hargitsa siyasar jihar ta hanyar karya da hasashe masu hatsari.
"Wannan na iya shafar zaman lafiyar jihar don haka ina son tabbatar da cewa ina nan daram-dam a APC.
"Ba ni da niyyar barin jam'iyyar a yanzu ko nan gaba," in ji mataimakin gwamnan cikin sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta ce mataimakin gwamnan yana da babban aiki a gabansa kuma yana can yana taya gwamna David Umahi ganin ya mika mulki cikin nasara.

"Ana kira ga yan mutane musamman yan APC su yi watsi da jita-jitar da wadanda ke adawa da jam'iyyar ke yada wa.

Kara karanta wannan

Wani shahararren gwamnan PDP: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba

"Wanda ke yada rahoton ya dena kuma ya nemi afuwar mataimakin gwamna nan take," sanarwar ta kara.

Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NRM, Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Kasa Da Yan Siyasan Arewa Sun Fice

A wani rahoton, kun ji cewa rikici ya barke a jam'iyyar National Rescue Movement (NRM) a yayin da yan siyasan arewa na jam'iyyar suka fice kan zargin wariyya daga takwarorinsu na kudu, Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Alhaji Abubakar Usman Jikamshi, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar a ranar Laraba a Abuja, yayin taron manema labarai, ya ce mafi yawancin mambobin kwamitin ayyuka, NWC, yan kudu maso gabas ne.

A cewarsa, shugaban jam'iyyar na kasa da sauran shugabannin ba su tuntubar mambobin jam'iyyar daga arewa a harkokin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel