Zaben fidda gwanin APC: Yadda deliget 17 suka mayar min da kudi na, inji Sanata

Zaben fidda gwanin APC: Yadda deliget 17 suka mayar min da kudi na, inji Sanata

  • Bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar APC, wani dan majalisar dattawa ya bayyana yadda taron ya kasance
  • A kalamansa, ya zargi gwamnan jiharsa da yin mai yiwuwa wajen dagula tsarin zaben jam'iyyar mai mulki
  • Ya bayyana cewa, akwai deliget 17 da suka mayar masa da kudinsa yayin da ya sha kaye a zaben na fidda gwani

Jihar Kogi - Dan majalisa mai wakiltar yankin Kwara ta tsakiya, Sanata Ibrahim Oloriegbe, ya ce wasu deliget da ya ba da kudade a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar sun mayar masa da abin sa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily inda ya yi magana kan rikicin da ke cikin jam’iyyar mai mulki.

Sanatan APC ya tona asirin wasu gwamnonin a zaben APC
Zaben fidda gwanin APC: Yadda deliget 17 suka mayar min da kudi na, inji Sanata | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wasu gwamnoni ne suka wawure komai a zaben fidda gwanin APC

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Sanata Oloriegbe ya caccaki tsarin da aka bi wajen gudanar da zabukan fidda gwanin da aka yi a wasu jihohin, inda ya zargi gwamnoni da kakaba deliget ga magoya bayan jam’iyyar, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Babu wani taron gangami; kamar a jiha ta, gwamna ne kawai ya zabo su (deliget) da daddare ya ce mun yi zabukan fidda gwani sai ga jeri ya fito. Don haka, ba ku ma san su waye deliget din ba… kuma hakan ya faru a jihohi da yawa.”
“Ko a inda ake cankar mutane, ya kamata a ba su ‘yancin yin amfani da ikonsu ta hanyar canko wanda suke so, amma abin ba haka yake ba.
“Gwamnoni sun zabo wadanda za su ba su umarni, wasu kuma sun yi rantsuwar kada kuri’a a inda gwamnonin ke so… kuma abin da ya faru ke nan a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

“A zabe na (na fidda gwani), wakilai 17 ne suka dawo don ba ni kudi na da na ba su na dawainiya; wasu kuma ba su dawo da shi ba, sun ce ‘muna so mu zabe ka ba, amma ba a ba mu damar kada kuri’a ba.
"Akwai wani abokin aikina a Kogi wanda ya ambata cewa mutane sun dawo masa da kudinsa."

Dan majalisar na cikin wasu da dama a majalisar dattawa da suka rasa tikitin jam’iyyarsu na komawa zauren majalisar dokokin kasar.

Yayin da wasun su suka fice daga jam’iyyar APC, wasu kuma wadanda ba su ji dadin lamarin ba sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin neman ya sa baki ga lamarin.

2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

A wani labarin, akalla mambobin jam’iyyar PDP 10,000 ne aka bayyana cewa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, an yi wannan biki na sauya sheka ne a filin shakatawa na Nelson Mandela da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Hon Wale Ojo, shugaban tsagin PDP na jihar, da Hon Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamnan PDP a zaben 2018 a Osun, na daga cikin wadanda suka fice daga PDP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel