Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NRM, Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Kasa Da Yan Siyasan Arewa Sun Fice

Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NRM, Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Kasa Da Yan Siyasan Arewa Sun Fice

  • Mataimakin shugaban jam'iyyar NRM na kasa, Alhaji Abubakar Usman Jikamshi ya yi murabus daga jam'iyyar
  • Jikamshi tare da wasu yan siyasan arewa sun fice ne kan zargin wariyya da rashin adalci da takwarorinsu na kudu maso gabas ke musu
  • A bangarensa, shugaban jam'iyyar na farko, Sanata Saidu Dansadau ya ce babu wani rikici a jam'iyyar kuma duk wanda ya ke son fita yana da yancin yin hakan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Gabanin babban zaben 2023, rikici ya barke a jam'iyyar National Rescue Movement (NRM) a yayin da yan siyasan arewa na jam'iyyar suka fice kan zargin wariyya daga takwarorinsu na kudu, Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Alhaji Abubakar Usman Jikamshi, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar a ranar Laraba a Abuja, yayin taron manema labarai, ya ce mafi yawancin mambobin kwamitin ayyuka, NWC, yan kudu maso gabas ne.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

Abubakar Jikamshi.
Rikici Ya Barke a Jam'iyyar NRM, Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Kasa Da Yan Siyasan Arewa Sun Fice. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, shugaban jam'iyyar na kasa da sauran shugabannin ba su tuntubar mambobin jam'iyyar daga arewa a harkokin jam'iyyar.

Ya ambaci taron jam'iyyar na kasa da aka yi a Maris da Yuni inda aka zabi shugaban jam'iyya na kasa, Isaac Chigozie Udeh, da dan takarar shugaban kasarta, Okwudili Nwa-Anyajike duk daga yankin Kudu maso Gabas ta hanyar da bata dace ba wanda ya saba wa demokradiyya.

Jikamshi, wanda shine dan takarar gwamnan jam'iyyar a zaben 2019 a Jihar Katsina ya ce abin ya saba wa tsarin demokradiyya.

Martanin shugaban jam'iyyar na farko

Da aka tuntube shi, shugaban jam'iyyar na farko, Sanata Saidu Dansadau, ya shaida wa Daily Trust cewa duk wanda ke son shiga ko fita daga jam'iyyar NRM ko wata daban yana da damar yin hakan.

"Muna masa fatan alheri; ba za mu hana kowa fita ba. Mun sha samun irin hakan har da wani tsohon shugaban kasa da ya yaga katinsa na jam'iyya ya kuma fita.

Kara karanta wannan

Abokin Takara: APC ta Dimauce, Tinubu ya Takaita Lalubensa a Borno, Kano, Kaduna

"Babu rikici a jam'iyyar mu, nasarar da muka samu a yan watannin da suka wuce abin yabawa ne," in ji Dansadau.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel