Babban Kuskuren da na Tafka Shine Zabar Atiku Mataimakina a 1999, Olusegun Obasanjo

Babban Kuskuren da na Tafka Shine Zabar Atiku Mataimakina a 1999, Olusegun Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, yace daukar Atiku matsayin mataimakinsa babban kuskure ne da ya tafka
  • Ya bayyana cewa, yana yin kuskure amma abu mafi muhimmanci shine yadda Ubangiji baya tozarta shi, yake kare shi
  • Tsohon sojan ya sanar da yadda Abacha yaso kama shi amma Amurka tace za ta bashi mafaka, ya ki amincewa, ashe alheri ne

Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo a ranar Asabar, yace zaben abokin tafiyarsa a zaben shugaban kasa na 1999 babban kuskure ne da ya tafka.

Channels Tv ta ruwaito cewa, ya yi wannan tsokacin ne yayin jawabi a garin Abeokuta a wani taron shugabanci da sana'o'in dogaro da kai wanda yayi da zababbun dalibai.

Kara karanta wannan

Peter Obi danmu ne amma Atiku za mu yi a kudu maso gabas – Ekweremadu

Obasanjo ya ci zaben shugabancin kasa na 1999 da 2003 tare da Alhaji Atiku Abubakar.

Abubakar ya zama 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar People's Democratic Party a zaben 2003.

"Ban ce ba na kuskure ba, ina yin su da yawa," Obasanjo yace.
"Amma abu daya dake faruwa da ni shine Ubangiji bai taba tozarta ni ba. Wannan shine abinda yafi muhimmanci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A misali, daya daga cikin kura-kuran da na tafka shi ne zabar na biyu na lokacin da zan zama shugaban kasa.
"Amma saboda kuskure ne mai inganci, Ubangiji ya tsare ni daga shi."

TheCable ta ruwaito cewa, Obasanjo, sojan da ya kai mukamin janar sannan yayi ritaya, yace mutane da yawa suna tunanin shiga aikin soja kuskure ne.

"Ko lokacin da Abacha yaso kama ni, ambasadan Amurka yace zasu kama ni kuma Amurka tace za ta bani mafaka. Nace a'a, zan dawo gida.

Kara karanta wannan

Yobe North: Abin Da Yasa Muka Tura Wa INEC Sunan Ahmad Lawan, Shugaban APC, Adamu

"Da wannan ya zama kuskure shima saboda da na rasa rayuwata.
"Abubuwa da yawa da na yi kuskure, amma Ubangiji ya kare ni daga su duka."

A bamu shugaban majalisar dattawa da na jam’iyya: Yankin Yarbawa sun gabatar da sharadin zaben Atiku

A wani labari na daban, jigogin Jamiyyar Peoples Democratic Party PDP na yankin kudu maso yamma sun gabatar wa uwar jam’iyya da dan takarar kujerar shugaban kasarta, Atiku Abubakar, abubuwan ya kamata yayi musu alkawari don ya samu kuri’u masu tsoka daga yankin.

Wannan ya biyo bayan jawabin cewa da yiwuwan jam’iyyar ta sha a kyar a yankin kasancewar dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, dan yankin ne.

Majiyoyi a jam’iyyar PDP sun bayyana cewa nasarar Tinubu a zaben fidda gwanin APC ya daburta lissafinsu a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel