A bamu shugaban majalisar dattawa da na jam’iyya: Yankin Yarbawa sun gabatar da sharadin zaben Atiku

A bamu shugaban majalisar dattawa da na jam’iyya: Yankin Yarbawa sun gabatar da sharadin zaben Atiku

  • Yankin Kudu maso yamma sun baiwa Atiku shawara kan abinda zai yi idan yana son ya samu kuri’un su
  • Mutan yankin Yarabawa sunce fitowar Tinubu ya daburtawa jam’iyyar PDP a yankin su
  • Asiwaju Bola Tinubu shine dan takarar da ake ganin zasu fafata da Alhaji Atiku Abubakar

Jigogin Jamiyyar Peoples Democratic Party PDP na yankin kudu maso yamma sun gabatar wa uwar jam’iyya da dan takarar kujerar shugaban kasarta, Atiku Abubakar, abubuwan ya kamata yayi musu alkawari don ya samu kuri’u masu tsoka daga yankin.

Wannan ya biyo bayan jawabin cewa da yiwuwan jam’iyyar ta sha a kyar a yankin kasancewar dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, dan yankin ne.

Majiyoyi a jam’iyyar PDP sun bayyana cewa nasarar Tinubu a zaben fidda gwanin APC ya daburta lissafinsu a yankin.

Wasu jigogin PDP a yankin sun baiwa Atiku shawarar wasu abubuwan da ka iya janyo hankalin mutane su zabesa.

Sun ce idan har Atiku na taka rawar gani a kuri’un yankin, toh wajibi ne a basu wasu mukamai maso lagwada.

Misali, Kakakin jam’iyyar PDP na jihar Oyo, Akeem Olatunji, a hira da manema labarai ya bukaci a baiwa Bayarabe kujerar Shugaban majalisar dattawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

“Muna sa ran za a baiwa yankin kudu maso yamma kujerar Shugaban majalisar dattawa.”

Amma tsohon mataimakin Shugaban uwar jam’iyyar, Diran Odeyemi, yace kujerar Shugaban uwar jam’iyyar suke bukata.

Odeyemi yace da kamar wuya PDP ta tabuka nasara a yankin tunda Tinubu bayarabe ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel