Kai Na Kowa Ne, Kuma Kai Ba Na Kowa Bane: Tinubu Ya Yabawa Buhari Kan Zaben Fidda Gwani

Kai Na Kowa Ne, Kuma Kai Ba Na Kowa Bane: Tinubu Ya Yabawa Buhari Kan Zaben Fidda Gwani

  • Bola Tinubu ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ya nuna halin girma da dattako yayin zaben fidda gwanin jam'iyyar tare da marawa dukkan 'yan takarar baya
  • Jigon kuma jagora ya yi godiya ga Buhari a kan yadda bai fifita wani 'dan takara a kan wani ba, tare da nuna duk matsayin su daya a wurinsa
  • Daga karshe, yayi godiya ga wakilan zaben jam'iyyar da shugabannin jam'iyyar tare da alkawarin dorawa daga inda Buhari ya tsaya gami da gini a kan turbar gaskiya da rikon amana

Bola Tinubu, 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, ya kambama shugaban kasa Muhammadu Buhari kasancewarsa "tsaka tsakiya" yayin zaben fidda gwanin jam'iyyar.

Kamar yadda wata takarda da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar a ranar Asabar, Tinubu ya jinjinawa Buhari.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Muhmmadu Buhari tare da Bola Ahmed Tinubu
Kai Na Kowa Ne, Kuma Kai Ba Na Kowa Bane: Tinubu Ya Yabawa Buhari Kan Zaben Fidda Gwani. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A takardar, a Adesina yace, Tinubu ya siffanta Buhari a matsayin "shugaban na kwarai, 'dan uwa kuma aboki," tare da jinjinawa nuna halin girma da ya yi wanda ya taimaka matuka wajen gudanar da zaben fidda gwanin cikin kwanciyar hankali.

"Ranka shi dade, dole hankalinka, tunani, natsuwa da halin dattakon da ka nuna na saura makwanni da watanni zaben tsaida 'dan takarar jam'iyyar mu mai albarka ya birge mutum.
"A matsayinmu da 'yan takara da jagororin jam'iyyar, muna rokonku gaba daya da ku zabi magajinku," kamar yadda takardar ta nuna.
"Dama tuntuni, ana saran haka musamman a damakaradiyyar Afirka. Har zuwa 6 ga watan Yuni, 2022, ranar da APC tayi zaben tsaida 'dan takarar shugaban, gaba daya Najeriya, duk da ni kaina muna jiran ka sanar da 'dan takararka. Dukkan mu mun yi zato kuma mun yi imani wannan abu ne mai sauki.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

"Sai dai, zaben fidda gwanin ne kadai ya sanar cikin daren, yayin 'yan takara suka iso filin zaben tare da jawabi, na ji dadi kuma na yaba da matsayarka kasancewarka tsaka-tsakiya ba tare da ka fifita wani daga cikin mu ba. A matsayina na 'dan takarar da ya fara magana, na samu damar magana tare da sauraro ba tare da wani abu ya dauki hankali na ba.
"Bayan shudewar wasu awanni a wannan yammacin, na gane cewa dukkanmu 'yan takarar da kake so ne. Yayin da ka nuna hakan a wasikar da ka rubuto min, shekarar 2013 da 2014 shi ne lokacin da muka samar tare da gina APC na nan don dukkan mu mu gani.
"Mai girma shugaban kasa, yayin da daren 6 ga watan Yuni ya rikide ya koma safiyar 7 ga watan Yuni, na matukar yabawa tare jin dadin matsayarka. "Kai na kowa ne a jam'iyyar kuma kai ba ka bin bayan wani daga cikin 'yan takarar jam'iyyar ka ke ba." Shugaban na kwarai, 'dan uwa kuma aboki.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

"Zan tsaya a nan tare sake gode maka bisa tsaya mana gaba daya da kayi. Da izinin Ubangiji da kuma shugabancin ka, jagoranci da goyon bayan ka, ina da tabbacin za mu mulki jam'iyyarmu , APC har zuwa yin nasara a zaben watan Fabrairu 2023. Za mu bi bayan nasarorin ka. Za mu gina ginshikanmu na bayyana gaskiya da dattako, wanda ka jagoranta."

Tinubu ya yi godiya ga wakilan zabe da sauran shugabannin jam'iyyar bisa goyon bayansu yayin zaben fidda fidda gwanin, inda ya kara da cewa kasancewarsa mai rike da tutar jam'iyyar nasara ce ga dukkan mambobin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel