Da duminsa: Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukuma ta farko a zaben gwamnan Ekiti

Da duminsa: Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukuma ta farko a zaben gwamnan Ekiti

  • 'Dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam'iyyar PDP, Bisi Kolawale ya lashe zabe a karamar hukumar Efon ta jihar
  • Bisi ya yi nasarar samun kuri'u 6,303, yayin da Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 4,012, sai Segun Oni na SDP mai kuri'u 339
  • Sakamakon karamar hukumar Ikere ta jihar Ekiti ya fito ne daga cibiyar tattara sakamakon zabe ta jihar kamar yadda suka sanar

Ekiti - Jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe zaben gwamna jihar Ekiti da ake yi na karamar hukumar Efon ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda sakamakon da aka sanar ya bayyana daga cibiyar tattara sakamakon zaben, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 4,012, 'dan takarar jam'iyyar PDP, Bisi Kolawole ne ya doke da shi wanda ya samu kuri'u 6,303 yayin a Segun Oni na jam'iyyar SDP ya samu kuri'u 339.

Kara karanta wannan

Da duminsa: APC ta Lashe Zabe a Karamar Hukuma ta Farko a Ekiti

Bisi Kolawale
Da duminsa: Jam'iyyar PDP ta lashe karamar hukuma ta farko a zaben gwamnan Ekiti Hoto: thecbaleng
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani labarin kuwa, Jam'iyyar APC mai mulki ta tabbata wacce ta lashe zaben gwamna jihar Ekiti da ake yi na karamar hukumar Ikere ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda sakamakon da aka sanar ya bayyana daga cibiyar tattara sakamakon zaben, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 12,086, 'dan takarar jam'iyyar PDP, Bisi Kolawole ne ke biye da shi wanda ya samu kuri'u 3,789 yayin a Segun Oni na jam'iyyar SDP ya samu kuri'u 1,934.

Asali: Legit.ng

Online view pixel