Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

  • Wani malamin addini, Fasto John Desmond, ya magantu kan jita-jitan da ake yadawa cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu zai dauki Musulmi don suyi takara
  • Fasto Desmond ya bayyana cewa wasu da ke kokarin bata sunan Tinubu ne ke ta yayata zancen domin tun farko aka kashe wannan maganar
  • Ya kuma bukaci dan takarar na APC da ya zabi mataimakin shugaban kasa a tsakanin kiristocin arewa don ba marada kunya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban kungiyar matasa masu sana’a ta Najeriya, Fasto John Desmond, ya bukaci yan bangar siyasa da su daina yada jita-jitan cewa Musulmi da Musulmi za a tsayar a jam’iyyar All Progressives Congress(APC) mai mulki.

Faston ya ce ana yada jita-jitan ne don bata sunan dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma yi masa lakabi da mai kishin addini, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto
Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Desmond a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, ya ce Tinubu na da wayo sosai da zai zabi nagari a matsayin abokin takara wanda zai kais hi ga nasara idan lokacin ya zo.

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Yan Najeriya mutane ne masu son addini da siyasa. Dukkanmu muna mutunta kanmu da addininmu, tun bayan da muka samu yancin kai.
“Batun yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa Musulmi da Musulmi ya mutu tun da farko kuma wadanda ke hasashen haka suna shiryawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zagon kasa ne.
“Kasancewarsa mutum mai dinke baraka, Asiwaju ya san illar tikitin Musulmi da Musulmi. Mutanen da ke shafawa APC bakin fentu makiyan Najeriya ne kuma lissafin siyasarsu ba zai yi aiki ba.”

Jaridar ta kuma kawo cewa Desmond ya yi godiya ga gwamnonin Arewa da suka ce lallai sai an mika mulki zuwa kudu, yana mai cewa hakan yana nuna nasarar da APC za ta samu a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

An yi kutse a shafin NNPC na Twitter, an yi amfani da shi wajen hasashen abokin takarar Tinubu

Desmond ya bukaci Tinubu da ya zabi dan arewa kirista domin ya baiwa masu yi ma siyasarsa bita da kulli kunya.

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

A gefe guda, mun ji cewa nan da ranar Juma’a dole kowace jam’iyyar siyasa za ta gabatarwa hukumar INEC sunayen ‘yan takararta a zaben shugaban kasa na 2023.

Punch ta kawo rahoto cewa mafi yawan jam’iyyun da za su shiga zaben 2023 su na kokarin ganin sun gama lissafinsu kafin wa’adin da aka bada ya kure.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta ce ba za ta kara lokacin gabatar mata da sunaye ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel