Shugaban kasa a 2023: A shirye nake na yiwa Tinubu aiki kamar yadda na yiwa Lawan – Orji Kalu

Shugaban kasa a 2023: A shirye nake na yiwa Tinubu aiki kamar yadda na yiwa Lawan – Orji Kalu

  • Sanata Orji Kalu ya bayyana kudirinsa na yin aiki don nasarar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a zaben 2023
  • Kalu ya sha alwashin yiwa Tinubu aiki kamar yadda ya yiwa shugaban majalisar dattawa, Lawan Ahmed kafin da lokacin zaben fidda dan takarar jam'iyyar
  • Tsohon gwamnan na jihar Abia ya kuma nuna gamsuwa da sakamakon zaben fidda dan takarar shugaban kasar na APC da aka yi a Eagle Square

Abuja - Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Kalu, ya ce zai yi aiki don nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Cif Bola Tinubu, a zaben 2023.

Kalu ya fada ma manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, cewa zai yiwa Tinubu aiki kamar yadda ya yiwa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kafin da lokacin zaben fidda gwanin APC.

Kara karanta wannan

Ban hakura ba fa: Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa, in ji Yaha ya Bello

Bola Tinubu tare da Orji Kalu
A shirye nake na yiwa Tinubu aiki don ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023 – Orji Kalu Hoto: Punch
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Abia wanda ya nuna gamsuwa da gudanarwa da sakamakon zaben fidda gwanin, ya bayyana cewa yayi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar zai fito ta hanyar maslaha.

Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto cewa Kalu ya dauki alkawarin aiki don nasarar Tinubu a zaben.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa ya gamsu cewa jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwanin

Ya ce:

“Ba don zaben fidda gwanin ba da jam’iyyar ta rabu biyu.
“Abu na gaba shine yiwa APC da dan takarar APC aiki; bamu da wani zabi. Ni dan jam’iyya ne kuma bana dauke ido kan batutuwa.
“Yanzu, yadda na yiwa Lawan yaki haka zan yiwa Bola Ahmed Tinubu yaki.”

Ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kin marawa kowani dan takarar shugaban kasa baya.

Kara karanta wannan

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

Jaridar The Sun ta kuma rahoto cewa Kalu ya nuna yakinin cewa kudu maso gabas za su zabi APC a 2023.

Ya ce:

“A kullun zan tsaya tsayin daka kan kowani lamari. Na yarda cewa Bola Tinubu ya lashe zabe kuma dukka jam’iyyar ta yarda da haka.
“Babu shakku game da nasarar sa, kuma da babu shakku kan nasararsa, ya zama dole mu fita filin daga mu yi aiki don nasarar jam’iyyarmu.
“Ina addu’a cewa mazabata, yankin kudu maso gabas, za su bamu wannan yardar da suka ba Shugaba Buhari a 2019, wanda ya bashi kaso 68 cikin 100 na kuri’u.
“Ina fatan za su ba APC wannan adadi na kuri’u."

Tikitin Musulmi-Musulmi: Kiristoci na da kariya saboda matar Tinubu fasto ce, inji Orji Kalu

A baya mun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu, ya tsoma baki a cece-kuce da ake ta yi kan batun tsayar da dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa daga addini guda.

Kara karanta wannan

Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari

Ana dai ta kai ruwa rana tun bayan da alamu suka nuna jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na iya tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin yan takararta na kujerar shugabancin kasar.

Yayin da kungiyar kiristocin Najeriya ta yi watsi da shawarar sannan ta gargadi jam’iyyu a kan haka, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya da su mayar da hankali kan cancanta fiye da akida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel