Ban hakura ba fa: Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa, in ji Yahaya Bello

Ban hakura ba fa: Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa, in ji Yahaya Bello

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana cewa, zai ci gaba da bin burinsa har zuwa zabe na gaba a 2027
  • Yahaya Bello ya bayyana hakan ne bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati
  • Ya kuma bayyana neman goyon baya ga Tinubu, inda ya ce magoya bayansa su mara masa baya a fafutukar

Abuja - Channels Tv ta rahoto cewa, gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Yahaya Bello, ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Wannan kenan kamar yadda ya lura cewa burinsa na yin shugabanci a 2023 ya ci tira kuma ya yi "gwajin makirufo ne kawai."

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

Bello zai sake tsayawa takara a 2027
Ban hakura ba: Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa, in ji Yahaya Bello | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Bello, wanda ya samu kuri’u 47 a zaben da aka gudanar a makon da ya gabata ya bayyana hakan ne ga ‘yan jaridun fadar gwamnatin kasa jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

A cewarsa, ya zo ne domin ganin shugaban kasar a ziyarar godiya da ya kawo masa na damar shiga wannan atisayen zaben da aka kammala.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya lura cewa kokarinsa na kwanan nan don neman tikitin shine "gwajin makirufo," ne kawai, ya kara da cewa kaokarinsa na gaba zai zama cike da hankoro mai kyau.

A kan farautar nemo abokin takarar Tinubu, ya lura cewa cancanta ya kamata a sa a gaba fiye da komai.

Ya ce game da batun tikitin musulmi-Musulmi ko Kiristanci-Kirista, babban abin da za a yi la’akari da shi na zaben ya kamata shi ne cancanta.

Kara karanta wannan

Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari

Ga magoya bayansa, Bello ya roki a ci gaba da ba shi goyon baya a takararsa na shugaban kasa yana mai cewa "wani lokacin ka ci nasara wani lokacin kuma ka sha kaye."

Ya bukace su da su goyi bayan mai rike da tutar APC a yanzu, wato Bola Ahmad Tinubu a zaben badi mai zuwa.

Atiku ya shiga ganawa da Gwamnonin PDP kan zabo abokin takararsa

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya shirya wani taron tattaunawa da gwamnonin da aka zaba a dandalin jam’iyyar PDP na kasar nan.

Taron wanda aka fara a baya kadan, an shirya shi ne domin kawo karshen shirin zabar wanda zai tsaya takara tare da Atiku.

Jaridar Vanguard ta ce ta samu sanarwar taron da Sakatariyar kungiyar Gwamnonin PDP ta fitar, wanda ke dauke da sa hannun Darakta-Janar na PDP GF, CID Maduagbanam.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel