Babbar magana: Gwamnan APC ya fusata, ya kori kwamishinansa na kudi saboda dalilai

Babbar magana: Gwamnan APC ya fusata, ya kori kwamishinansa na kudi saboda dalilai

  • Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya kori daya daga cikin kwamishinoninsa saboda rashin aiki kamar yadda doka ta tanada
  • Ya bayyana korar kwamishinan ne a yau dinnan, inda ya nemi ya tattara kayansa ya bar ofishin na gwamnati
  • A cewar sanarwar da ke tabbatar da korar ta sa, gwamnan ya ce, kwamishinan ya gaza wajen sauke hakkin da ke kansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya dakatar da kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arziki na jihar, Mista Orlando Nweze bisa zargin "kasa gudanar da aikinsa yadda ya kamata".

Sanarwar dakatarwar dai ta samu sa hannun sakataren gwamnatin jihar Dr Kenneth Ugbala, kuma aka ba manema labarai ranar Laraba a Abakaliki, The Nation ta ruwaito.

Gwamna Umahi ya kori kwamishinan kudi
Da Dumi-dumi: Gwamnan APC ya fusata, ya kori kwamishinansa na kudi saboda dalilai | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gwamnan ya umarci Nweze da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga sakataren dindindin na ma’aikatar kafin karshen ranar Laraba 15 ga watan Yuni.

Da muka gani daga Daily Trust ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Don Allah, ka tabbatar da bin wannan umarnin."

Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet

Idan ka taba aiki na kwana daya a rayuwar ka kuma ka bari, to tabbas watakila ka taba rubuta takardar murabus dinka cikin salon da aka saba dashi.

Wani kuma ya zo da salo, ya mika takardar murabus dinsa mai kalmomi uku masu sauki wadanda suka bar jama'ar soshiyal midiya baki bude.

Rayuwar aiki dai na da wahala. Don haka, lokacin da kake da shugaba mai ba ka wahala ko yanayin aiki mara dadi, sha'awar yin murabus a kowace rana wani abu ne da ka iya zuwa kwakwalwarka.

Mutumin mai amfani da shafin Twitter @MBSVUDU ya yada kwafin wasikar murabus din wanda kawai ta ce "Bye bye sir," kalaman da ke nufin bankwana da mai gidansa.

2023: Buhari ya tura doguwar wasika ga gwamnonin APC don nemawa Tinubu alfarma

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran ‘ya’yan jam’iyyar su hada kai domin tabbatar da nasarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Buhari, a wata wasika da ya aike wa shugaban gwamnonin, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, ya ce Tinubu ba bako bane a idon gwamnonin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar da sashen wasikar a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel