An Kori Lakcarorin Najeriya 2 Saboda Tafka 'Manyan' Laifuka a Jami'a

An Kori Lakcarorin Najeriya 2 Saboda Tafka 'Manyan' Laifuka a Jami'a

  • Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Ozoro ta kori wasu malamai biyu daga aiki saboda samunsa da wasu laifuka
  • An kori Dr Bassy A. Ekanem da Dr Jacob A. Meye saboda karyar yin wani bincike kan jirgi mara matuki, bawa dalibai makin karya, karbar kudi, almubazaranci da zamba yayin jarrabawa ta kwamfuta
  • Jami'ar ta kore su ne bayan kwamitin ladabtar da malamai ta yi bincike da same su da laifin don haka ta ce an sallame su kuma ana fatan hakan ya zama darasi ga wasu

Jihar Delta - Mahukunta a Jami'ar Kimiyya da Fasaha, Ozoro, Jihar Delta sun sallami malamai biyu daga aiki kan zargin damfara na karatu.

The Punch ta rahoto cewa hakan na kunshe ne cikin sanarwa da jami'ar ta fitar da manema labarai suka gani a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yankewa 2 daga abokan harkallar Abba Kyari hukunci

Taswirar Jihar Delta
Jami'ar Delta Ta Kori Lakcarori 2 Saboda Tafka 'Manyan' Laifuka. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce an kori malaman ne bayan samunsu da karyar "yin bincike kan kere jirgi mara matuki, zamba wurin jarrabawar kwamfuta, karbar kudi daga dalibai, almubazaranci da bada sakamakon karya ga dalibai."

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Ana sanar da jami'ar cewa kwamitin koli a taronta da aka saba yi a ranar Laraba 8 ga watan Yunin 2022, ta amince da shawarwarin kwamitin ladabtar da ma'aikata inda aka kori lakcarori biyu Dr Bassy A. Ekanem da Dr Jacob A. Meye nan take.
"Idan za a iya tunawa an same su da hannu wurin karyar kere jirgi mara matuki, kwafen aikin wasu, ikirarin mallakar hakkin jirgi mara matuki, zamba wurin jarrabawar kwamfuta, kwacen kudi, almubazaranci da bada sakamakon karya ga dalibai.
"Don haka, an same su da laifin saba ka'idar aiki, kama daga karya wurin yin binciken da aka ambata, an kore su daga jami'ar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

"Wannan sanarwar ta shafi kowa musamman wadanda ke aiki a jami'ar, kuma ana fatan zai zama izina ga saura."

Asali: Legit.ng

Online view pixel