2023: Buhari ya tura doguwar wasika ga gwamnonin APC don nemawa Tinubu alfarma

2023: Buhari ya tura doguwar wasika ga gwamnonin APC don nemawa Tinubu alfarma

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga gwamnonin jam'iyyar APC domin wata bukata
  • Ya bayyana cewa, ya kamata gwamnonin su hada kai domin ganin Tinubu ya lashe zaben 2023 mai zuwa
  • Shugaban ya bayyana haka ne a wasikar da ya tura wa gwamnan jihar Kebbi, shugaban kungiyar gwamnonin APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran ‘ya’yan jam’iyyar su hada kai domin tabbatar da nasarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Buhari, a wata wasika da ya aike wa shugaban gwamnonin, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, ya ce Tinubu ba bako bane a idon gwamnonin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar da sashen wasikar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara

Buhari ya rubuta wasikar neman goyon baya ga gwamnonin APC a madadin Tinubu
2023: Buhari ya tura doguwar wasika ga gwamnonin APC game burin Tinubu na gaje shi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cikin wasikar, Buhari ya yaba wa gwamnan jihar Kebbi, wanda ya kasance shugaban kwamitin zaben fidda gwanin da aka kammala, bisa kwarewa da kuma yadda ya gudanar da zaben fidda gwanin cikin lumana, rahoton Blueprint.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu zai daura daga inda na tsaya, Buhari

Shugaban ya ce yana fatan yin aiki da gwamnonin domin ganin Tinubu ya lashe zaben 2023.

‘’A yau a matsayina na dan jam’iyyar APC mai kishin kasa kuma mai ruwa da tsaki, na yi imanin za ku hada kai da dan takararmu domin ganin ya ci zabe a 2023.
‘’A shekaru 7 da suka gabata a gwamnati, mun samu nasarori da dama. Duk da haka, muna da abubuwa da yawa da za mu yi. Aikin APC ya yi nisa don haka muna bukatar dukkan ku da ku hada kai don ganin dorewar ci gaban tafiyarmu ta zaman lafiya da ci gaba."

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

A wani labarin, kungiyar yakin neman zaben Yahaya Bello na neman shugaban kasa ta caccaki fitowar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni mai taken, ‘Yahaya Bello ne dai gwarzon wadanda aka zalunta.'

A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Yemi Kolapo, ya fitar kuma Legit.ng ta gani, ya bayyana atisayen zaben fidda gwnain APC a matsayin wani tsari da aka samu matsala a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.