Mataimakin Tinubu: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 7 a Aso Rock

Mataimakin Tinubu: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 7 a Aso Rock

  • Yayin da jam'iyya mai mulki ke cigaba da faɗi tashin zakulo mataimakin shugaban ƙasa, gwamnonin sun dira fadar Buhari
  • Yanzu haka shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawar sirri da aƙalla gwamnoni Bakwai a fadarsa ranar Talata
  • Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, Gwamnonin Kaduna, Filato, Nasarawa, Imo, Kogi. Jigawa da Borno sun samu halarta

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga taron sirri yanzu haka da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko a APC, Gwamna Atiku Bagudu, na jihar Kebbi, shi ne ya jagoranci takwarorinsa zuwa wurin Buhari.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar APC ke cigaba da faɗi tashin zakulo mataimaki ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Ko shi zai zama mataimaki? Bola Tinubu ya sa labule da wani gwamnan Arewa a Abuja

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tare da gwamnoni.
Mataimakin Tinubu: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 7 a Aso Rock Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Mutanen da suka halarci taron

Taron wanda ke gudana yanzun ya samu halartar shugaban ma'ikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnati, Boss Mustapha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan kuma a ɗaya ɓangaren gwamnonin da suka je wurin taron sune, Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Abdullahi Sule na Nasarawa, Badaru Abubakar na Jigawa.

Sauran sune, gwamna Simon Lalong na jihar Filato, Yahaya Bello na jihar Kogi da kuma gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Channels TV ta ruwaito cewa duk da babu cikakken bayani kan dalilin taron amma ya zo ne mako ɗaya bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa.

Su wa ake tsammanin zaben mataimaki daga cikin su?

Rahoto ya nuna cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ya rubuta sunan tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, wanda ya taka rawa wajen nasararsa a matsayin wanda ya ke son ya zama mataimaki.

Kara karanta wannan

Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu

Mambobin tsohuwar jam'iyyar CPC da ta cure zuwa APC, suna shirin gabatarwa Buhari da sunan Abubakar Malami da Hadi Siriki don zaɓar ɗaya ya zama mataimaki.

Tsohon sakataren gwamnati, Babagana Kingiɓe, wanda ya kasance mataimaki ga MKO Abiola a zaɓen 1993 ya tura sunayen mutum uku ga Tinubu domin duba wa.

Mutanen sun haɗa da gwamna Babagana Umaru Zulum, mataimakiyar shugaban majalisar ɗinkin duniya, Amina J Muhammed, da kuma Kashim Ibrahim-Imam.

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APGA ya zaɓi wanda zai zama masa mataimaki a zaɓen 2023

Yayin da manyan jam'iyyu ke ta faɗi tashin neman mataimaki, Farfesa Umeadi, ya kawo karshen kace-nace a jam'iyyar APGA.

Ɗan takarar da jam'iyyarsa sun amince Kwamaret Muhammed Koli ya zama mataimaki yayin zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel