Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamna Yahaya Bello

Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamna Yahaya Bello

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, tare da tawagar wasu gwamnoni sun gana da takwaransu na jihar Kogi, Yahaya Bello
  • Gwamna Bello na daya daga cikin yan yakarar da suka sha ƙasa a hannun Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC
  • Rahoto ya nuna cewa an shirya taron ne da nufin kwantar da hankalin gwamna Bello, wanda ya fusata da sakamakon zaɓen

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC kuma tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka ya shiga taron sirri da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Masana siyasa na ganin hakan wani sashi ne a kokorin shawo kan fusatattun yan takarar da suka fafata da Tinubu a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Tinubu da Yahaya Bello.
Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamna Yahaya Bello Hoto: Alhaji Yahaya Bello/facebook
Asali: Facebook

Tinubu ya shiga taron ne tare da gwamnan Legas, Babajide Sanwo- Olu, gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da kuma gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya samu halartar wurin taron.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai babu wani cikakken bayani kan ko batun wanda zai zama mataimakin Tinubu a zaɓen 2023 na daga cikin Ajendar da za'a tattauna a wurin taron.

Jaridar da tattaro cewa manyan jiga-jigan jam'iyyar APC zasu zanta da manema labarai game da abun da suka cimma a wurin ganawar ta su idan suka fito.

Gwamna Bello ya ba Tinubu Ofishin Kanfe

Gwamna Yahaya Belloa ya ba da kyautar ofishin Kamfe ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamnan ya sanar da wannan kyauta yayin da Tinubu ya kai masa ziyara ranar Jumu'a 10 ga watan Yuni, 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Karon farko bayan lashe zaɓen APC, Tinubu ya lallaɓa ya sa labule da shugaban ƙasa

Da yake jawabi bayan haka, Bola Tinubu ya yaba da kokarin Belle tare da yin alƙawarin hana idonsa bacci don tabbar da haɗin kan jam'iyya da kuma kasa baki ɗaya.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun yi gaba da kusan miliyan N50m a Sakatariyar karamar hukuma

Wasu miyagun yan bindiga sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun aikata babbar ɓarna.

Bayanai sun nuna cewa m a haran sun sace shugaban matasan yankin, yayin da suka haɗa da Motoci masu tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel