Da dumi-dumi: Dan takarar gwamna na APC a jahar Bauchi ya fice daga jam'iyyar

Da dumi-dumi: Dan takarar gwamna na APC a jahar Bauchi ya fice daga jam'iyyar

  • Yan makonni bayan zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC, jam’iyyar mai mulki na ta fama da sauye-sauyen sheka
  • Na baya-bayan nan shine na dan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar Bauchi wanda ya sanar da ficewar daga APC
  • Sai dai kuma, Farouk Mustapha bai sanar da sabuwar jam'iyyar da zai koma ba gabannin zaben na 2023 mai zuwa

Bauchi - Dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi a zaben 2023, Farouk Mustapha, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, Mustapha ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar ne bayan kayen da ya sha a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

Tsohon shugaban hafsan sojin sama, Sadique Baba Abubakar ne dai ya lashe tikitin jam’iyyar mai mulki a zaben da aka yi na ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu.

Farouk Mustapha
Da dumi-dumi: Dan takarar gwamna na APC a jahar Bauchi ya fice daga jam'iyyar Hoto: Farouk Mustapha
Asali: Facebook

Sai dai kuma, dan siyasar wanda ya ce ba za su zamo abokan gaba da yan tsohuwar jam’iyyarsa ba koda sun hadu a bangaren adawa a zabe mai zuwa bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koma ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya wallafa a shafin nasa:

“Bayan dogon nazari da kuma shawara da 'yan-uwa da abokan huld'ar siyasa, na yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC.
“Ina matukar godiya ga shugabanni, da membobin jam'iyyar APC bisa ga dama da suka bani, na shiga jam'iyyar, har nayi takarar Gwamna a cikinta. Bazan manta da wannan halarci ba.
“Na shiga jam'iyyar APC ne domin bada gudumowa wajen kawo cigaba a Jahar Bauchi! Sai dai ban samu dai-daiton kudiri da shugabannin jam'iyyar ba. Hakan yasa na yanke shawarar sauya sheka zuwa wani waje domin cigaba da gwagwarmaya don inganta rayuwar al'ummarmu.

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

“Ina neman alfarmar 'ya'yan jam'iyyar APC dasu fahimce ni, domin ban kullaci kowa ba.
“Kuma duk da akwai yiwuwar mu kasance a bangarori masu hamayya da juna a lokacin zabe, hakan bazaisa mu zama abokan gaba ba.”

2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe

A wani labarin, wani bidiyo ya bayyana kuma ya shahara a shafukan soshiyal midiya inda aka nuno wani limamin katolika yana umurtan mambobin cocinsa da basu da katin zabe da su koma gida.

Masu amfani da shafin twitter da dama sun wallafa bidiyon, ciki harda dan fafutukar siyasa, Rinu Oduala, wanda shine kan gaba wajen rijistan katin zabe.

Limamin Katolikan ya yi jawabi ga dandazon mabiyansa a gaban cocin, yana mai cewa kada wanda ya damu da zuwa coci cikinsu idan har basu da katin zabensu a hannu, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng